Ko da yake ba a bude hanyar mota daga waje zuwa gundumar Wenchuan ba, wato tsakiyar wurin da ke shan wahalar girgizar kasa, amma rundunar sojoji da 'yan sanda masu dauke da makamai da yawansu ya kai dubbai sun riga sun shiga cikin gundumar Wenchuan ta hanyar jiragen sama, da jiragen ruwa, har da kafa, domin gudanar da aikin ceto.
Hafsan hafsoshi na wani divishin na rundunar sojojin 'yan sanda Mr. Wang Yi ya jagoranci sojoji dari biyu, sun yi tafiya da kafa kawai har kilomita 90 cikin awoyi fiye da 20, a ran 13 ga wata da daddare, sun shiga cikin gundumar Wenchuan domin gudanar da aikin ceto. Ya ce, ya kasance da bala'i mai tsanani a wurin. Ya ce,
'A halin da muke ciki, yawan jama'ar da suka ji rauni a birnin ya zarce dubu uku. Sulusin gidaje na birnin sun ruguje, sauran gidaje kuma sun lalata sosai, ba a iya kwana a cikinsu ba. Kauyukan da ke kan tsaunuka sun riga sun ruguje, ba a iya kididdiga yawan mutanen da suka bace da wadanda suka ji rauni ba, sakamakon matsalar hanya.'
Ban da wannan kuma, wata kungiyar likitanci da ke hada da mutane 30 sun riga sun shiga cikin gundumar Wenchuan, sun fara gudanar da aikin ceto kan mutanen da suka ji rauni a wurin.
A ran nan da yamma, firayin ministan kasar Sin Mr. Wen Jiabao ya yi rangandi kan bala'in a gundumar Wenchuan cikin jirgin sama. Ya gaya wa jama'a cewa, rundunar sojoji za ta yi kokarin da take iyawa domin gudanar da aikin ceto. Ya ce, 'Gwamnatin tsakiya ba ta manta da wannan wuri ba, tabbas ne za ta ceci jama'a daga girgizar kasa. Idan a ba iya bude hanyar mota ba, za a yi amfani da jiragen sama wajen daukar masu jin rauni zuwa waje, za a yi musu aikin ceto. A halin yanzu dai, muna kokari sosai wajen samun jiragen sama daga sauran wurare. A yau da safe, mun riga mun dauki mutane fiye da 50 da suka ji rauni daga wurin, za mu ci gaba da daukar masu jin rauni zuwa waje.'
1 2
|