A ran 13 ga wata da dare, hukumar ba da umurni wajen fama da girgizar kasa da kuma gudanar da ayyukan ceto ta sake kiran taro, inda firayim minista Wen Jiabao ya bukaci a ceto mutane cikin lokaci domin rage yawan mutanen da suka mutu ko suka jikata. Li Yun, wakilin kamfanin dillancin labarai na XinHua na kasar Sin da ke yin intabiyu a ofishin daidaita abubuwan da suka faru ba zato ba tsammani na babban sashen hafsoshi na rundunar sojan kasar Sin, cewa yanzu dimbin sojojin kasar Sin suna kwarara zuwa yankuna masu fama da bala'in na lardin Sichuan. Kuma ya kara da cewa, "Bisa kididdigar da aka yi, an ce, yawan sojojin da suka isa yankuna masu fama da bala'in ya kai kimani 16000, kuma yawan sojoji da ke kan hanya ya kai fiye da 34000, a ciki, sojoji 20000 sun iya iso wurin a ran 13 ga wata."(Kande Gao) 1 2
|