Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-05-14 17:57:38    
Kasar Sin tana gudanar da gagaruman ayyukan ceto a yankunan lardin Sichuan da ke fama da girgizar kasa

cri

Ya zuwa ran 13 ga wata, yawan mutanen da suka mutu sakamakon girgizar kasa da ta auku a lardin Sichuan na kasar Sin ya riga ya zarce 14000, yanzu kasar Sin tana yin iyakacin kokarinta wajen gudanar da gagaruman ayyukan ceto a yankunan da ke fama da bala'in. Sojojin ba da taimakon agaji sun riga sun shiga yankin da ke cibiyar girgizar kasa. To yanzu ga cikakken bayani.

Ko da yake nisan da ke tsakanin gundumar Wenchuan da ke cibiyar girgizar kasa da birnin Chengdu, hedkwatar lardin Sichuan ya kai fiye da kilomita 100 kawai, amma zaizayewar kasa daga tsaunuka da ta auku sakamakon girgizar kasa ta toshe hanyoyin zuwa gundumar Wenchuan, haka kuma sabo da mummunan yanayi da kuma kananan girgizar kasa da suka auku kullum, shi ya sa ayyukan ceto ke gamuwa da wahaloli sosai. Wakilinmu Liu Tao ya ruwaito mana labari daga birnin DuJiangyan da ke kusa da gundumar Wenchuan, cewa

"Idan ana son zuwa Wenchuan daga birnin Chendu, dole ne a wuce birnin Dujiangyan. Amma sabo da zaizayewar kasa daga tsaunuka, wasu kayayyakin agaji da aka samu daga lardin Sichuan da kuma gwamnatin kasar Sin ba su iya isa gundumar Wenchuan ba. A da ana neman daukar su ta jiragen sama masu saukar ungulu, amma sabo da ana ta yin ruwan sama a Dujiangyan da Chendu da kuma Wenchuan, shi ya sa ba a iya yin haka ba."

Kasa samun hanyoyin shiga gundumar Wenchuan matsala ce mafi tsanani da ake gamuwa da ita yanzu a cikin ayyukan ceto. Ba yadda za a yi sai mutane masu ceto sun shiga gundumar Wenchuan da kafafunsu daga yankunan da ke kewayen gundumar. A ran 13 ga wata da tsakar rana, sojoji na rukunin farko sun riga sun shiga garin Yingxiu na gundumar Wenchuan wajen ceton fararen hula da ke cikin kangaye. Daga baya kuma, sojoji da 'yan sanda fiye da 800 sun isa gundumar domin gudanar da ayyukan ceto. Bisa labarin da aka samu yanzu, an ce, dakuna da gidaje na gundumar sun lalace sosai, kuma an tabbatar da cewa, mutane 500 sun mutu, haka kuma halin da kauyen Longxi da garin Yingxiu da ke kusa ke ciki ya fi tsanani. Yanzu sojojin kasar Sin masu yawa suna kwarara zuwa gundumar Wenchuan bisa iyakacin kokarinsu. Firayim ministan kasar Sin Wen Jiabao ya bukaci bangarorin da abin ya shafa da su bude hanyoyin zuwa Wenchuan tun da wuri. Kuma ya kara da cewa, "Wannan girgizar kasa tana da matukar tsanani, kuma cibiyarta tana gundumar Wenchuan. Har yanzu ba a bude hanyoyin zuwa gundumar ba. Sojojin kasar Sin suna neman dabarun bude hanyoyin domin ceton mutanen da ke cikin kangaye. Za a samar da isassun sojoji bisa bukatun da aka yi."

1 2