Bayan saukarsa a wuraren da bala'in ya shafa, nan da nan firayim minista Wen Jiabao ya fara shugabanncin ayyukan yaki da bala'in don ceton jama'a. Ya bukaci hafsoshi da sojoji wadanda suka shiga ayyukan yaki da bala'i don ceton jama'a da su kawar da dukan wahalhalu da suke sha, ko da kafa ma su je wuraren da bala'in ya fi galabaita. Ya ce, " da farko a ceci jama'a, kuma a ceci jama'a musamman a wurare da cibiyoyin da bala'in girgizar kasa ya shafa da wuraren da ba a iya samun labarunsu. Ruwa a jallo a je wadannan wurare tun da wuri, idan an je wuraren tun da dakika daya, to, mai yiwuwa ne, za a ceci wani mutum."
A wuraren da bala'in ya shafa, firayim minista Wen Jiabao ya je asibitoci da makarantu da sauran wurare don kai ziyara ga jama'ar da bala'in ya galabaita, inda ya bayyana muku halin da ake ciki game da bala'in da kuma yadda ake yaki da bala'in don ceton jama'a. Ya ce, ma'aikata masu ba da agaji za su yi dukan abubuwan da suke iya yi wajen ceton jama'a.
Bayan aukuwar bala'in girgizar kasar, hukumar yaki da bala'I ta kasar Sin ta tashi tsaye ta aiwatar da harkokin yaki da bala'in cikin gaggawa. Ma'aikatar jin dadin jama'a ta kasar da ma'aikatar kudi ta kasar sun hada kansu don samar da kudin agaji da yawansu ya kai kudin Sin Yuan miliyan 200 ga wuraren Lardin Sichuan da bala'in ya shafa, ta yadda za a ba da agaji ga jama'a wajen kawar da wahalar da suke sha wajen zaman rayuwarsu. Da minti 35 na daddaren ranar yau, a karo ne na farko aka fara jigilar kayayyakin agaji daga kungiyar agaji wato Red Cross ta lardin Sichuan cikin gaggawa zuwa wurare da bala'in ya fi galabaita. Madam Zhang Bo, mataimakiyar shugabar kungiyar ta bayyana cewa, "yanzu, muna shirin jigilar wadannan kayayyakin agaji zuwa wurin Wenchen wanda bala'in girgizar kasa ya fi galabaita. Bisa labarun da muka samu, hanyar da ake bi zuwa wurin ya yanke, amma duk da haka za mu yi kokari zuwan can, don yin jigilar kayayyakin zuwa wurin. (Halilu) 1 2
|