Saurari
Jiya Litinin da yamma da karfe 2 da minti 28, an yi girgizar kasa mai tsanani da karfinta ya kai awo 7 da digo 8 bisa ma'aunin Richter a gundumar Wenchuan na lardin Sichuan da ke a kudu maso yammacin kasar Sin, girgizar kasar ta shafi sauran wurare, kuma an ji ta a larduna da jihohi da manyan birane sama da 10 na kasar Sin. Bisa kidayar da ma'aikatar jin dadin jama'a ta kasar Sin ta yi, an ce, ya zuwa karfe 7 na safiyar yau, wannan girgizar kasa ta yi sanadiyyar mutuwar mutanen da yawansu ya kai 9219 a lardunan Sichuan da Gansu da Shaanxi da birnin Zhongqing da sauran larduan da birane 4, haka kuma ta ruguje gidaje sama da dubu 50. Yanzu, gwamnatin kasar Sin na iyakacin kokari wajen yaki da bala'in girgizar kasa don ceton jama'a.
Gundumar Wenchuan wadda bala'in girgizar kasa ya fi galabaita yana da nisan kilomita sama da 100 daga birnin Chendu, fadar gwamnatin lardin Sichuan na kasar Sin. Yawan mutanenta ya wuce dubu 110. Bayan aukuwar girgizar kasa, Malam Zhang Hongwei, kakakin hukumar kula da harkokin girgizar kasa ta Sin ta bayyana wa kafofin watsa labaru cewa,
"wannan girgizar kasa mai tsanani ta shafi wurare masu fadi. An ji ta a jihohin Ningxia da Yunnan da Tibet da lardunan Gansu da Qinghai da Shanxi da Shaanxi da Shandong da Henan da Hunan da birnin Zhongqing da sauran wurare da yawa.
Bayan aukuwar girgizar kasar, nan da nan shugaba Hu Jintao na kasar Sin ya bukaci hukumomin da abin ya shafa su yi dukan abubuwa da suke iya yi wajen ceton masu jin raunuka, don tabbatar da tsaron rayukan jama'ar wuraren da bala'in ya shafa. Kasar Sin ta kafa hedkwatar yaki da bala'i da ceton jama'a, kuma firayim minista Wen Jiabao ya zama babban kwamandanta. Firayim minista Wen Jiabao kuma ya tashi zuwa wuraren da bala'in ya shafa ba tare da jinkiriba don shugabancin ayyukan yaki da bala'I don ceton jama'a.
1 2
|