Irin wannan ra'ayi almara ce kawai da ke yaduwa a tsakanin fararen hula. Makomar Hu Xueyan tana da nasaba da shi kansa da kuma dalilin zamanin da. Bayan rasuwarsa, an taba sayar da gidan Hu Xueyan sau da dama, gidan ya lalace sosai a sakamakon karancin kwaskwarima. A farkon shekarar 1999, hukumar birnin Hangzhou ta tsai da kudurin yin kwaskwarima kan gidan Hu Xueyan. A watan Janairu na shekarar 2001, an sake bude kofar gidan Hu Xueyang ga masu yawon shakatawa. yanzu masu yawon shakatawa fiye da dubu 190 sun kawo wa wannan tsohon gida ziyara a ko wace shekara.
Saboda hukumar Hangzhou ta bi ka'idar yin kwaskwarima kan tsoffin gine-gine ta hanyar da aka saba bi a zamanin da, shi ya sa ta maido da kayayyakin tarihi yadda suke kasancewa a zamanin da, ta kuma kubutad da wannan muhimmin gini na gargajiya, wato gidan Hu Xueyan, wanda ke kasancewa misali mai kyau a fannin samun nasarar yin kwaskwarima kan gine-ginen gargajiya, haka kuma, shi ne alamar Hongzhou ta fuskar tarihi da al'ada. 1 2
|