Masu sauraro, barkanku da war haka, barkanmu da sake saduwa da ku a cikin shirinmu na yawon shakatawa a kasar Sin. Ni ce Tasallah da mu kan samu a ko wace rana Talata. A tarihin kasar Sin mai tsawon dubban shekaru, an yi ta samun mashahurran mutane. Bayan dogon lokaci, wuraren da wadannan mutane suka taba zama, kuma suna kasancewa har zuwa yanzu sun zama wuraren yawon shakatawa masu sigogin musamman. Yau ma bari mu kai ziyara ga gidan Hu Xueyan, inda za mu kara saninmu kan zaman rayuwar wannan dan kasuwa na zamanin daular Qing na kasar Sin, wato yadda ya taba zama yau da shekaru fiye da dari 1 da suka wuce.
Tsohon gidan Hu Xueyan yana cikin birnin Hangzhou na lardin Zhejiang a gabashin kasar Sin. A shekarar 1872, Hu Xueyan, wani dan kasuwa na wurin ya yi amfani da dimbin kudade domin gina wani babban gida mai fadin murabba'in mita dubu 5 da dari 8 ko fiye. An fi mai da hankali kan kayayyakin gine-gine, kuma an gina wannan babban gida bisa nagartacciyar fasaha. Gidan Hu Xueyan ya zama kyakkyawan misali na gidajen masu kudi na yankunan Jiangsu da Zhejiang a zamanin daular Qing na kasar Sin, yana kuma kasancewa matsayin koli a tsakanin gidajen mazauna na Hangzhou, a kan mayar da shi tamkar gida mafi kyau na dan kasuwa a karshen zamanin daular Qing na kasar Sin. Mr. Wang Li da ke aikin jagorantar masu yawon shakatawa domin yin ziyara a tsohon gidan Hu Xueyan ya yi karin bayani da cewa,'A farkon lokacin ransa, Hu Xueyan ya gudanar da harkokin kasuwanci, daga baya, ya zama wani jami'i kamar mataimakin minista a yanzu. A lokacin can, kudaden da Hu Xueyan ya samu ya kai rabin kudaden shiga da mahukuntan zamanin daular Qing suka samu a shekara guda.'
Hu Xueyan ya yi shekaru 3 daidai yana gina wannan babban gidansa. Gidansa yana da kusurwoyi 4, an raba shi zuwa rassa 4 bisa amfaninsa.
Yanzu mutanen da ke zama a kusa da gidan Hu Xueyan su kan kai ziyara ga wannan tsohon gida tare da abokansu da suka zo daga sauran wuraren kasar. Liu Lei, wani mazaunin wurin ya jagoranci abokansa domin ziyarar gidan Hu Xueyan, ya gaya mana cewa,'Na taba kawo nan ziyara har sau 3. A ko wane karon da na kawo nan ziyara, na kan gayyaci abokaina da mu ziyarci wannan tsohon gida tare, inda mu kan kalli gine-ginen gargajiya na kasar Sin da kuma kara saninmu kan tarihin kasar Sin. Ko da yake yawancin rassan gidan aka gina su a zamanin yanzu, amma ba a bambance su da sauran rassan gidan ba. An gina sabbin rassan gidan ta hanyar da aka bi a zamanin da.'
Ko da yake Hu Xueyan ya taba samun dukiyoyi masu tarin yawa kusan a duk ransa, amma makomarsa ba ta da kyau ko kadan. Bayan da ya yi shekaru 10 ko fiye yana zama a cikin wannan babban gida, ya yi hasarar dukkan dukiyoyinsa. Wasu suna ganin cewa, dalilin da ya sa Hu ya yi hasarar kudadensa shi ne domin bai taki sa'a ba. Mr. Wang Li ya yi mana bayani da cewa,'Hu Xueyan na kasancewa wani dan kasuwa da kuma wani jami'in mahukuntan zamanin daular Qing. Shi ya sa a lokacin da ya gina babban gidansa, ya iya sayen duk wurin da yake bukata, a ciki har da kusurwa ta arewa maso yamma. Bisa mukaminsa da kuma dukiyoyinsa, in ya tilasta ko kuma ya yi toshiyar baki, ya iya sayen kusurwar arewa maso yamma ta wannan wurin da yake so. Amma akwai wani shagon wanzami a wannan kusurwa, wanzamin ya ki sayar da shagunsa, wanda ya gada daga kaka kakaninsa, kuma kasuwa ta ci sosai a shagon wanzami. Hu Xueyan yana tsammanin cewa, in wanzamin ba ya so, to, shi ke nan, sun iya kulla kyakkyawar makwabtaka a tsakaninsu. A karshe dai, mazaunan Hangzhou su kan ce, sa'a ta soma gudu daga wajen Hu Xueyan, ya fara yi hasarar kudadensa daga wannan kusurwar arewa maso yamma.'
1 2
|