Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-05-12 21:03:54    
Jihar Hainan ta zama babban wurin samar da kayayyakin lambu da ya'ya itatuwa a kasar Sin

cri

Malam Chen Yongwang, kakakin hukumar kula da aikin noma ta jihar Hainan ya bayyana cewa, a shekarun 1990, gwamnatin jihar ta tsaida manufar bunkasa aikin noma iri na wuri mai zafi ta hanyar zamani don ba da kwarin gwiwa ga manoma da su kara bunkasa aikin noman kayayyakin lambu da 'ya'yan itatuwa. Sa'an nan gwamnatin jihar ta nuna himma wajen ba da hidima ga aikin noma ta hanyar kimiyya. Malam Xu Quan, shugaban wani wurin ba da hidima ga aikin noma a fannin kimiyya da fasaha na jihar ya bayyana cewa, "wurinmu ya kan shirya kos don horar da manoma sau daya ko biyu a ko wane wata. Alal misali muna horar da su wajen rigakafin kwari da kuma kashe su, sa'an nan muna sanar da su labarin bala'in kwari kafin aukuwarsa. Haka kuma muna horar da su wajen noman kumkumba da yaji da sauransu ta hanyar zamani."

Malam Chen Yongwang, kakakin hukumar kula da aikin noma ta jihar Hainan ya kara da cewa, tun daga shekarar 1998, jihar ta kan shirya bikin baje kolin amfanin gona a ko wace shekara. Yawan amfanin gona da ake sayarwa bisa yarjejeniyoyin cinikayyar da aka daddale a gun bikin ya kan kai tan miliyoyi a ko wace shekara. Don haka gwamnatin jihar ta dauki matakai daban daban don jagorancin manoma da su bunkasa aikin noma ta hanyar kimiyya. Ya ce, "gwamnatin jihar ta kan shirya manyan kamfanonin aikin noma da su yi bincike a saurarn wurare waje da tsibirin a ko wace shekara, don gano bukatun da ake yi a kasuwanni. Bisa sakamakon binciken da aka samu, an gabatar da shawarwari kan yawan kayayyakin lambu da za a noma, ta yadda manoma za su daidaita shirinsu na aikin noma." (Halilu)


1 2