Jihar Hainan da ke a kuriyar kudancin kasar Sin, wuri ne mai zafi, inda ake samun kayayyakin lambu da 'ya'yan itatuwa masu armashi. Yanzu kuma ta riga ta zama babban wurin da ake samar da kayayyakin lambu da 'ya'yan itatuwa ga kasar Sin. Ba ma kawai jihar Hainan tana samar da amfanin gona ga manya da matsakaitan birane na babban yankin kasar Sin da yawansu ya wuce 100 ba, har ma tana sayar da shi zuwa Amurka da kungiyar tarayyar Turai da Rasha da Japan da shiyyar kudu maso gabashin Asiya da sauran kasashe da shiyyoyi sama da 20. Yawan muhimmin amfanin gonar da dukkan jihar ta sayar wa kasashen waje ya kai kimanin Tan miliyan 4.5, yawan kudin da ta samu ya wuce dalar Amurka miliyan 400. Yanzu, bunkasa aikin noma na wuri mai zafi ta hanyar zamani ya riga ya zama daya daga cikin manyan tsare-tsaren bunkasa harkokin tattalin arzikin jihar Hainan.
A karshen karni na 20, daga binciken da ya yi, Malam Guo Zhiyao, mutumin jihar Henan ta kasar Sin ya gano cewa, kayayyakin lambun da ake samu a tsibirin Hainan suna da inganci sosai, don haka zasu sami karbuwa a kasuwannin babban yankin kasar, sa'an nan ya dau niyyar zuba jari a tsibirin. Ya ce, "kafin zuwana, daga binciken da na yi a kan kasuwannin sayar da amfanin gona na babban yankin, na gano cewa, sabo da ana samun isasshen hasken rana a tsibirin Hainan, kuma ko a yanayin dari ma ana zafi a wurin, shi yasa kayayyakin lambun da ake samu a tsibirin suna da kyau sosai, farashinsu kamar yaji da yalo da kankana da sauransu ya fi na jihar Guangdong tsada. Bayan haka na fara zuba jari a tsibirin."
Malam Guo Zhiyao ya fara zuba jari a jihar Hainan a shekarar 1999, ya kafa wani kamfanin raya aikin noma. A karkashin jagorancinsa, manoman wurin sun noma kayayyakin lambu don biya bukatun da ake yi a kasuwannin babban yankin kasar. Ta haka kamfaninsa ya sami bunkasuwa sosai, yana sayar da kayayyakin lambu da 'ya'yan itatuwa zuwa Faransa da Jamus da Canada da kuma sauran kasashe.
1 2
|