Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-05-06 18:07:34    
Shirin samar da gidaje ya kyautata muhallin zama ga manoma makiyaya na Tibet

cri

Ban da kyautata gidajen kwana ga manoma da makiyaya, shirin samar da gidajen kwana da ake aiwatarwa ya kuma inganta manyan ayyuka a kauyuka makiyayan Tibet, kuma an yi ta kyautata ayyukan samar da ruwa da wutar lantarki da hanyoyi da sadarwa da dai sauransu a wurin, zaman rayuwar manoma da makiyaya ya sami kyautatuwa a zahiri. An ce, a shekarar da muke ciki, jihar Tibet za ta kara zuba kudin Sin biliyan 1 da miliyan 400 da kuma miliyan 860 wajen gyaran hanyoyi da kuma ayyukan samar da wutar lantarki a makiyayai na Tibet.

Mataimakin shugaban jihar Tibet, Yang Haibin ya nuna yabo sosai ga shirin nan na samar da gidaje. Ya ce,"Tun bayan da aka 'yantar da jihar Tibet a shekarar 1951, ma iya cewa, shirin ya kasance matakin da aka fi zuba kudaden jari kuma matakin da ya fi amfana wa manoma makiyaya. Bayan da aka shafe tsawon shekaru biyar ana aiwatar da shirin, za a gyara fuskar makiyayar Tibet kwarai da gaske"

Shirin nan na samar da gidajen kwana ya kuma sami karbuwa sosai daga wajen manoma da makiyaya na wurin, kuma iyalin madam Tsamjor da ke gundumar Doilungdeqen ta birnin Lhasa na daya daga cikinsu. A watan Maris na shekarar da muke ciki, Madam Tsanjor tare da iyalanta sun kaura cikin sabon gida, wanda ko kudin Sin fen daya ma ba ta kashe ba. Game da sabon gidan, Madam Tsanjor ta gamsu sosai, ta ce,"Gwamnati ta ba da kudin taimako yuan dubu 36 a kan gidan, matalauta kamar mu na iya zama cikin sabon gida irin wannan alheri ne da gwamnati ta ba mu. Kullum mamata na gaya mini, babu zama mai dadi kamar haka kafin a 'yantar da Tibet, kuma dalilin da ya sa muka sami zama mai kyau a yanzu shi ne sabo da kyawawan manufofin gwamnati."(Lubabatu)


1 2