Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-05-06 18:07:34    
Shirin samar da gidaje ya kyautata muhallin zama ga manoma makiyaya na Tibet

cri

Tun daga shekarar 2006, an fara aiwatar da shirin samar da gidajen kwana a kauyuka da makiyaya da ke jihar Tibet mai cin gashin kanta ta kasar Sin, don kyautata muhallin zama ga manoma da makiyaya. Ya zuwa yanzu dai, sakamakon shirin, manoma da makiyaya dubu 570 sun sami gidajen kwana masu inganci. Ban da wannan kuma, shirin ya kyautata manyan ayyuka a wurin, ciki har da ayyukan samar da ruwa da wutar lantarki da kuma hanyoyi, ya kuma samar da damar kara samun kudin shiga ga manoma da makiyaya na wurin.

Daga cikin mutane sama da miliyan 2 da dubu 800 a jihar Tibet, kashi 80% sun kasance manoma da makiyaya. Sakamakon makeken fili a wurin da kuma mugun yanayin kasa, muhallin zama a baya yake ga manoma da makiyayan. Don neman gyara halin da ake ciki, tun daga shekarar 2006, jihar Tibet ta fara aiwatar da shirin samar da gidaje, wanda ya fi mai da hankali a kan gyaran gidajen kwana a kauyuka da tsugunar da makiyaya. Bisa shirin, daga shekarar 2006 zuwa ta 2010, za a gyara gidaje ga iyalan manoma da makiyaya kimanin dubu 220, ta yadda kashi 80% na manoma da makiyaya mazauna Tibet za su iya samun gidaje masu inganci. Lhagpa Phuntshogs, babban darektan cibiyar nazarin harkokin Tibet ta kasar Sin, ya bayyana cewa, shekaru biyu da ake aiwatar da shirin samar da gidaje, an riga an cimma manyan nasarori."Shekaru fiye da biyu da ake aiwatar da shirin samar da gidaje, gaba daya aka zuba kudaden jarin da yawansu ya wuce kudin Sin yuan biliyan 6 da miliyan 600, kuma manoma da makiyaya dubu 570 sun sami sabbin gidaje, muhallin zama na manoma da makiyaya ya sami kyautatuwa kwarai da gaske, kuma fadin gida ga kowanensu ya kai muraba'in mita 36.4, wanda ya karu da muraba'in mita 16.8 kafin a aiwatar da shirin."


1 2