
An yi karin bayani da cewa, an raba furannin Peony zuwa tsare-tsare 9 bisa launukansu, kamar ja da fari da rawaye da shudi da baki da kore da sauran launuka 3, haka kuma akwai ire-iren furannin fiye da 1100. Furen Peony ya riga ya zama shahararriyar alama ce ta birnin Luoyang mai tsawon shekaru dubbai.
A lokacin da mutane ke yawo a wurin yawon shakatawa na Wangcheng, sun gano cewa, wasu furannin Peony sun riga sun yi toho, dubban furannin suna da matukar kyan gani, sun yi kama da takara da juna domin kara nuna kyan gani. A ko ina a wannan wurin yawon shakatawa, ana iya ganin kyawawan furannin Peony da suke yin toho sosai. Masu yawon shakatawa da suka zo daga wurare daban daban na kasar Sin suna yawo a tsakanin tekun furannin, wasu sun dauki hotuna, sun ji dadin kallon irin wadannan kyawawan furanni da kuma fahimtar zuwan lokacin bazara.

Za a yi gasar wasannin Olympic a karo na 29 a Beijing a wannan shekara, mazauna birnin Luoyang suna fatan furannin Peony za su kara bai wa gasar wasannin Olympic ta Beijng haske.(Tasallah) 1 2
|