Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-05-06 15:25:03    
Jin dadin kallon furannin Peony a birnin Luoyang na lardin Henan na kasar Sin

cri

Masu karatu, watakila ba ku sani ba, a lokacin yanzu, wato watan Afrilu na ko wace shekara, a birnin Luoyang na lardin Henan da ke yankin tsakiya na kasar Sin, wanda sarakuna na zamanin dauloli 9 na da na kasar Sin suka mayar da shi tamkar babban birnin mahukuntansu, dimbin furannin Peony da aka dasa a gefunan tituna da wuraren yawon shakatawa sun yi toho daya bayan daya. Haka kuma, masu yawon shakatawa da yawa sun kai wa Luoyang ziyara domin more idanunsu da irin wadannan furanni masu matukar kyan gani.

Ko da yake masu yawon shakatawa da suka kai wa Luoyang ziyara suna iya ziyarar kogunan dutse na Longmen da gidan ibada na Baimasi da na Guangdimiao da sauran wuraren gargajiya, amma sun fi nuna sha'awa kan furannin Peony masu launuka daban daban.

Furen Peony ya shahara a kasar Sin tun can da, a kan mayar da shi tamkar sarkin furanni. A matsayinsa na garin wannan kyakkyawan fure, birnin Luoyang ya fara noman furannin Peony tun daga zamanin daular Sui, wato yau da shekaru 1500 ko fiye da suka wuce.

A shekarar da muke ciki, hukumar birnin Luoyang ta yi bikin kaddamar da kallon furannin Peony a shahararren wurin yawon shakatawa na Wangcheng a wurin. Daga nan ne mutane suka iya more idanunsu da kyawawan furannin Peony a yankunan birnin da bayan birnin da kuma yankin babban tsaunin da ke kudancin birnin daya bayan daya a cikin wata guda ko fiye.


1 2