Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-04-30 20:44:33    
Wurare daban daban na kasar Sin sun yi farin ciki da maraba da ranar da ta kai kwanaki 100 da suka rage don kira wasannin Olimpic na Beijing

cri

A yau da safe kuma, an shirya gudun Marathon a cibiyar wasannin Olimpic ta Beijing. Jama'a da yawansu ya kai kusan dubu da wasu masu kishin dogon gudu na kasashen waje sun halarci aikin. An kuma shirya sauran aikace-aikacen murna. Wani mutum da ya zo daga yankin Tongzhou ya yi farin ciki da bayyana cewa, maraba da wasannin Olimpic wani burinmu ne, tun daga ranar 13 ga watan Yuli na shekarar 2001 da birnin Beijing ya yi nasarar samun damar shirya wasannin Olimpic har zuwa yanzu, a kowace shekara muna shiga gasar gudun Mrathon.

Ban da birnin Beijing, sauran biranen kasar Sin su ma sun shirya aikace-aikacen murna ta hanyoyi daban daban. A reshen filin wasan kwallon kafa na birnin Qinhuangdao da ke arewacin kasar Sin, wakilan jama'ar birnin da yawansu ya kai dubu 3 sun halarci aikace-aikacen da aka shirya don taya murna. Wani malamin da ya riga ya yi ritaya ya rubuta wata rubutaciyyar waka da ke da lakabi haka: "Wasannin Olimpic, a shriye muke a kodayaushe", Malamin nan mai suna Jing Guofang ya bayyana cewa, a wannan lokaci, muna farin ciki muna jin nishadi, muna son morewar farin ciki da wasannin Olimpic ya kawo mana tare da jama'ar duk duniya, don cim ma mafarkinmu gu daya, a shriye muke a kodayaushe.

Jama'a masu sauraro, abin da kuka saurara shi ne wakar da ake rera da ke da lakabi haka: Muna shirye. 

Kabilu daban daban na Jihar Tibet su ma sun mai da hankulansu ga wasannin Olimpic, kuma a ko'ina a jihar Tibet, ana iya ganin halin da ake kasancewa cikin farin ciki da nishadi. A ranar 30 ga watan Afril, jama'a fiye da dubu 3 na jihar Tibet su ma sun shirya aikace-aikacen murna.(Halima)


1 2