Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-04-30 20:44:33    
Wurare daban daban na kasar Sin sun yi farin ciki da maraba da ranar da ta kai kwanaki 100 da suka rage don kira wasannin Olimpic na Beijing

cri

Yau ranar 3o ga watan Afril, kuma rana ce ta kwanaki 100 da suka rage don soma wasannin Olimpic na Beijing na shekarar 2008. Birnin Beijing da sauran birane na kasar Sin sun shirya aikace-aikacen murna ta hanyoyi daban daban, mutane sun yi farin ciki da maraba da zuwan wasannin Olimpic.

Yau da safe, a babban dakin taruwar jama'a na birnin Beijing, an shirya taron tayar da himma ga wasannin Olimpic na shekarar 2008 a rana ta kwanaki 100 da suke rage don soma wasannin Olimpic. Shugaban majalisar ba da shawara ga harkokin siyasa ta kasar Sin Jia Qinglin ya halarci taron.wakilan da suka zo daga rukunonin zamantakewar al'umma wajen likitanci da ba da ilmi da wasan motsa jiki na birnin Beijing su fiye da dubu 6 sun halarci taron.

A gun taron, shugaban kwamitin wasannin Olimpic na birnin Beijing Mr Liu Qi ya gabatar da ayyukan da kwamitin wasannin Olimpic na Beijing da sassa daban daban na Beijing za su yi da hakkin da ke bisa wuyansu a kwanaki 100 masu zuwa. Ya bayyana cewa, ya kamata a sa kaimi ga aikin hidima da za a yi ga wasannin Olimpic da wasannin Nakasassu na birnin Beijing da kuma kara karfi ga ilmantar da mazaunan Beijing wajen bin da'a da wayewar kai, tare kuma da kara karfin hadin guiwa da ke tsakaninsu da kwamitin wasannin Olimpic da kwamitin wasannin nakasassu na kasashen duniya, da kuma yin namijin kokarin aiki don shirya wasannin Olimpic da ke da halayen musamman bisa babban matsayi.

Wakilan masu sa kai kuma masu ba da hidima ga wasannin Olimpic na jami'ar Beijing sun yi rantsuwa a gun babban taron, inda suka nuna cewa, tabbas ne za su ba da hidima sosai ga bakin gida da na waje. Na sa kaina ga wasannin Olimpic na Beijing da na nakasassu na Beijing, kuma za mu yada ruhun wasannin Olimpic, kuma za mu aiwatar da tunanin ba da hidima, mu tinkari zuwa gaba cikin himma da kwazo tare da ba da hidima cikin farin ciki, mu yi hadin guiwa ba da taimakon juna, mu yi namijin kokari da kuma bayyana halinmu na sadaukar da rai da sada zumunci da nuna kaunar juna da taimakon juna don samun sakamako ga kasar mahaifa da kuma kara abubuwa masu kyau ga wasannin Olimpic, murmushin da masu sa kai suke yi zai zama katin suna mai kyau ga birnin Beijing.

1 2