Bayan makwanni shida, manazarta sun gano cewa, jikin mata da suka yi wasan yoga ya sami sauki, kwarewarsu wajen yawo da hau matakalu da daukar abin nauyi sun fi kyau idan an kwatanta su da na kungiyar daban. Wasu matan da suka kamu da ciwon sankarar mama sun bayyana cewa, bayan da suka yi wasan yoga, ba su ji gajiya sosai ba yayin da suke samun hutu sosai cikin barci.
Makasudin yin wasan yoga shi ne karfafa tankwaruwar masu yin wasan ta yin motsi sannu sannu, kuma su samu sakin jiki ta kyautata numfashinsu. Darussan wasan yoga da manazarta suka shirya suna da sauki a gwargwado, ta yadda mata da ke fama da ciwo ba za su sha wahalar yin wasan yoga ba. Kuma manazarta sun bayyana cewa, za su ci gaba da yin bincike domin tabbatar da cewa, dalilin da ya sa mata masu fama da ciwon sankarar mama suka sami sauki shi ne domin wasan yoga ko amfanin hankalin mutane. 1 2
|