Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-04-30 17:26:03    
Babban malamin wasan Piano na kasar Sin mai suna Yin Chengzong

cri

Tsibirin Gulangyu shi ne wurin da ya yi tamkar yadda wani gadon jinjiri na koyon ilmin Piano yake, amma ba a iya samun malaman da ke kwarewa sosai wajen koyar da ilmin Piano, in ana son zama mai kwarewar kada Piano, to dole ne a bari wurin, kodayake a wancan lokacin, ba a iya samun motocin daukar fashinja da jiragen ruwa da jiragen sama da jiaragen kasa ba,amma ya shiga cikin babbar mota ya yi tafiya ta kwanaki hudu, sa'anan kuma ya shiga cikin jirgin kasa ya isa birnin Shanghai. Ya ce, wannan muhimmin mataki ne da ya dauka, idan ban fita waje, to, kada Piano zai zama sha'awa gare ni kawai.

A jami'ar koyar da ilmin wake-wake da kide-kide ta birnin Shanghai , Mr Yin Chengzong ya soma koyon ilmin kada Piano a hukunce, bayan wasu shekarun da aka yi masa horo cikin mawuyacin hali, sai ya sami sakamako mafi kyau. A shekarar 1959, ya sami Lambawan wajen gasar kada Piano da aka shirya a birnin Viena a bikin samarin duniya, bayan shekaru biyu da suka wuce, ya sami damar yin dalibta a birnin Moscow, a shekarar 1962, Mr Yin Chengzong ya kuma sami lambatu wajen gasar kada piano ta Tchaikovsky ta kasa da kasa. Ya bayyana cewa, a wancan lokaci, gwamnatinmu ce ta tura ni zuwa kasar Rasha don yin karatu. A lokacin, kasar Rasha ta kai matsayin koli wajen nuna wasannin fasaha, saboda haka wannan na da amfani sosai gare ni.

Bayan da ya koma gida daga birnin Moscow, tsohon shugaban kasar Sin Mao Tsedong ya gana da shi, kuma ya yi masa himma cewa, ya kamata ya kara tsara kide-kiden gargajiyar kasar Sin , daga nan sai Mr Yin Chengzong ya soma gyara wasu shahararrun kide-kiden wasannin kwaikwayo da kide-kiden gargajiyar kasar Sin don su zama wadanda za a iya kada su ta hanyar yin amfani da Piano. A shekarar 1969, bisa shugabancinsa ne aka tsara kidan "Yellow River Concerto" da aka kada ta hanyar yin amfani da Piano.

Don tsara kidan nan, Mr Yin Chengzong ya yi aiki tare da masu tuka jiragen ruwa a bakin rawayen kogi , a lokacin kusancin karshen tsara kidan, Yin Chenzong bai taba fita waje har cikin kwanaki uku, kuma a kowace rana, ya ci abinci a karo daya kawai, kafin an nuna wasan kada kidan, yatsar hannu na Yin Chengzong ya kamu da ciwo, amma bai lura da wannan sosai ba, a karshe dai ya sami babbar nasara wajen wasan kada Piano . A cikin shekaru fiye da goma, Yin Chengzong ya kan kada kidan nan. A shekarar 2005, a ranar cika shekaru 60 da samun nasarar yakin kin Fasist a duniya, kasashe fiye da 50 suka nuna wasannin kada kidan nan na Piano.

A shekarar 1983, Yin Chengzong ya kaura zuwa kasar Amurka . Kidan da ya kada ya jawo hankulan mutanen da suke wucewar tagogin gidansa.

A kasar Amurka sau biyu ne Mr Yin Chengzong ya shirya taron nuna wasannin kada Piano shi kadai, kafofin yada labarai sun bayyana cewa, shi ne nagartaccen dan wasan Piano na kasar Sin mafi kyau sosai. (Halima)


1 2