Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-04-30 17:26:03    
Babban malamin wasan Piano na kasar Sin mai suna Yin Chengzong

cri

Mr Yin Chengzong shi ne tsohon hannun wasan Piano da ke da shekaru 67 da haihuwa. A lokacin da ya soma cika shekaru goma da haihuwa, ya sami babbar lambar yabo a gasar nuna wasannin Piano da aka shirya a kasa da kasa. A shekaru 50 zuwa shekaru 60 na karnin da ya shige, ya gabatar wa jama'ar kasar Sin kide-kiden zamani aru aru na kasashen yamma , a sa'i daya kuma ya kada kide-kiden gargajiyar kasar Sin ta hanyar yin amfani da Piano, kuma ya sami sakamako mai kyau sosai.

A shekarar 1941, an haifi Mr Yin Chengzong a tsibirin Gulanyu na birnin Xiamen da ke bakin teku a kudu maso gabashin kasar Sin , a lokacin da can, wurin nan wuri ne da kasashen waje suka haya shi. A lokacin da Yin Chengzong yake karami, ya kan ji kide-kiden da aka yi daga majami'a, daga nan sai ya soma wayewar kansa wajen koyon ilmin kide-kide, in da ya sami dama, sai ya mai da hankali sosai wajen saurarar kide-kiden da aka kada ta hanyar yin amfani da Piano, wani lokaci ya zauna ya saurari kide-kiden da aka kada ta hanyar yin amfani da Piano har cikin yini daya. Dayake ya rasa sharadi mai kyau, shi ya sa bai iya samun taimako daga wadanda ke da fasahar kada Piano , amma bisa hazikancinsa ne ya iya kada Piano ta hanyar koyonsa na kansa .Sa'anan kuma, bisa zugar da wani malamin kide-kide na garinsa ne , Yin Chengzong da ke da shekaru 12 da haihuwa ya tsai da kudurin zuwa birnin Shanghai don ci gaba da koyon ilmin kada Piano, amma hanyar nan mai wuyar bi ta canja duk rayuwarsa.

1 2