Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-04-30 08:39:47    
Sha'anin yawon shakatawa na Beijing ya riga ya shirya aikinsa a gun gasar wasannin Olympic

cri

Kazalika, kamfanonin yawon shakatawa daban daban na Beijing sun kafa wasu sabbin hanyoyin bude ido musamman, a gun gasar wasannin Olympic, za a gabatar da littafin yin bayani kan wadannan hanyoyin yawon shakatawa ga 'yan wasa masu shiga gasar wasannin Olympic. Babban manajan babban kamfanin yawon shakatawa na duniya na kasar Sin Yao Yuecan ya bayyana cewa:  "Mun yi kokarin kafa sabuwar hanyar yawon shakatawa, muna fatan masu yawon shakatawa daga gidan kasar Sin da kasashen waje za su kalli karfin sabon Beijing da sabuwar gasar wasannin Olympic da idonsu. "

Mataimakin magajin birnin Beijing Ding Xiangyang ya bayyana cewa, gasar wasannin Olympic ta samar wa bunkasuwar sha'anin yawon shakatawa na Beijing wani inzi mai kyau, kamata ya yi birnin Beijing ya yi amfani da shi, ta haka kuma sha'anin yawon shakatawa na Beijing zai shiga wani sabon mataki. Ya ce:  "A yawancin birane wadanda suka shirya gasar wasannin Olympic, yawan masu yawon shakatawa ya kan karu bisa babban mataki. Shi ya sa ya fi kyau mu yi amfani da wannan dama mu yi kokari don ciyar da sha'anin yawon shakatawa na birnin Beijing gaba."(Jamila Zhou)


1 2