Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-04-30 08:39:47    
Sha'anin yawon shakatawa na Beijing ya riga ya shirya aikinsa a gun gasar wasannin Olympic

cri

Gasar wasannin Olympic gaggarumin bikin wasannin motsa jiki ne, shi ma gaggarumin bikin yawon shakatawa ne. An kimanta cewa, a gun gasar wasannin Olympic ta Beijing, yawan masu yawon shakatawa da za su zo birnin Beijing domin bude ido zai kai fiye da miliyan daya. Ran 10 ga wata, shugaban hukumar yawon shakatawa ta Beijing ya bayyana cewa, sha'anin yawon shakatawa na Beijing ya riga ya shirya aikin karbar masu yawon shakatawa a gun gasar wasannin Olympic, tabbas ne Beijing zai biyan bukatun ba da hidima ga masu yawon shakatawa a gun gasar wasannin Olympic. A cikin shirinmu na yau, bari mu kawo muku bayani kan wannan.

Ran 10 ga wata, hukumar yawon shakatawa ta kasar Sin da gwamnatin birnin Beijing da kwamitin shirya gasar wasannin Olympic na birnin Beijing sun yi babban taron share fage kan sha'anin yawon shakatawa na Beijing musamman domin maraba da gasar wasannin Olympic, inda aka tsara shiri kan aikin karbar masu yawon shakatawa a gun gasar wasannin Olympic. Shugabar hukumar yawon shakatawa ta Beijing madam Zhang Huiguang ta yi mana bayani cewa,  "Domin maraba da gasar wasannin Olympic, Beijing ya kara mai da hankali kan aikin gina gine-ginen ba da hidima ga jama'a, a sa'i daya kuma, ya kara kyautata muhallin yawon shakatawa, ta haka kuma ingancin ba da hidima ya sami kyautatuwa a bayyane."

Ban da wannan kuma, a gun gasar wasannin Olympic, Beijing ya tsai da cewa, za a gayyaci masu yawon shakatawa daga kasashen waje da su shiga gidajen mutanen birnin domin su yi zaman rayuwa tare, ana kiran aikin da suna 'iyalin gasar wasannin Olympic'. Game da wannan, shugaban sashen kula da hotel da abinci na hukumar yawon shakatawa ta Beijing Zhou Shuqi ya ce:  "Iyalin gasar wasannin Olympic iyali ne wanda zai samun damar karbar 'yan kallon kasashen waje. Za mu zabi iyalai wajen dubu daya da su karbi masu yawon shakatawa daga kasashen waje a cikin gidansu a gun gasar wasannin Olympic. Makasudin aikin nan shi ne domin samar da dama ga masu yawon shakatawa daga kasashen waje da su duba zaman rayuwar jama'ar birnin Beijing da idonsu kai tsaye. Mun hakake cewa, masu yawon shakatawa daga kasashen waje za su yi maraba ga wannan."

1 2