Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-04-29 16:53:33    
Lardin Fujian yana dukufa kan kyautata tsarin shigad da mazauna cikin inshorar jiyya

cri

Bisa kididdigar da aka yi, an ce, ya zuwa karshen shekarar da ta gabata, mazauna kusan dubu 700 na biranen Fuzhou da Xiamen kuma Nanping sun shiga inshorar jiyya da kuma samun gatanci ga ake bayarwa a fannin samun jiyya. Madam Chen Xiang da muka ambata a baya ita ce daya daga cikinsu. Jiang Gengsheng, shugaban cibiyar gudanar da inshorar zaman al'umma ta birnin Xiamen ya bayyana cewa, hukumar kula da inshorar zaman al'umma ta gwamnatin wurin za ta biya kudaden da wadanda suka shiga inshorar jiyya suka kashe wajen ganin likita da yawansu ya kai kashi 40 zuwa kashi 60 cikin dari, kuma ana sa ran cewa, hukumar za ta kara yawan kudaden da suka biya a nan gaba. Kuma ya kara da cewa, "Game da mutanen da suka shiga inshorar jiyya, a bayyane ne an rage yawan kudaden da suka kashe wajen samun jiyya. Bisa kididdigar da muka samu, an ce, game da kwanta a asibiti don samun jiyya, yawan kudaden da aka rage ya kai kashi 47 cikin dari ga tsoffi, kuma ya kai kashi 55 cikin dari ga yara. Lalle wannan ya kawo wa fararen hula alheri a zo a gani." (Kande Gao)


1 2