Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-04-29 16:53:33    
Lardin Fujian yana dukufa kan kyautata tsarin shigad da mazauna cikin inshorar jiyya

cri

Assalamu alaikum, jama'a masu sauraro, barkanku da war haka. Barkanmu da sake saduwa a wannan fili na "kimiyya da ilmi da kuma kiwon lafiya na kasar Sin". Ni ce Kande ke gabatar muku da wannan shiri. A cikin shirinmu na yau, bari mu leka tsarin shigad da mazaunan birane da gundumomi cikin inshorar jiyya da ake gudanarwa a lardin Fujian da ke kudu maso gabashin kasar Sin, wanda ya ba da tabbaci sosai ga jama'a wajen samun jiyya.

Madam Chen Xiang da shekarunta ya kai fiye da 80 da haihuwa tana da zama a birnin Xiamen na lardin Fujian. A farkon shekara ta 2006, an tabbatar da cewa, ta kamu da sankarar hanji. Wannan cuta mai tsanani da ta kamu da ita ba zato ba tsammani ta kara nauyin da ke bisa wuyan gidanta wajen tattalin arziki. Zheng Zhenzhen, matar dan Madam Chen Xiang da ke kula da ita ta gaya mana cewa, "Lalle cutar da take kamuwa wani babban nauyi ne da ke bisa wuyanmu. Ni da mijina dukkanmu ba mu da aikin yi, kuma yanzu ana bukatar yawan kudade wajen ganin likita, shi ya sa idan ba a iya mayar da kudaden da muka kashe wajen jiyya, to ba mu da karfi wajen biyan kudaden asibiti."

Lokacin da suke damu da yadda za su iya tattara yawan kudaden jiyya, tsarin shigad da mazaunan birane da gundumomi cikin inshorar jiyya ya ba su haske.

Wakilinmu ya samu labari cewa, a shekara ta 2001, lardin Fujian ya fara kafa tsarin shigad da ma'aikata na birane da gundumomi cikin inshorar jiyya da kuma tsarin jiyya na hadin gwiwa irin na sabon salo na kauyuka a wurare daban daban, ta haka an warware matsalar ganin likita da ma'aikata da 'yan kauyuka ke fuskanta. Domin shigad da dukkan mazaunan lardin cikin tsarin ba da tabbaci ga zaman al'umma wajen samun jiyya, a shekarar da ta gabata, lardin Fujian ya fara gabatar da tsarin shigad da mazaunan birane da gundumomi cikin inshorar jiyya a biranen Fuzhou da Xiamen da kuma Nanping. Lai Shiqing, mataimakin shugaban hukumar kula da kwadago da ba da tabbaci ga zaman al'umma ta lardin Fujian ya gaya mana cewa, "Tsarin shigad da mazaunan birane da gundumomi cikin inshorar jiyya wani tsari ne da aka kafa bisa kudaden da gwamnati da kuma fararen hula suka tattara tare domin warware matsalar kwanta a asibiti da kuma ganin likita da mutanen da ke shiga inshorar ke fuskanta lokacin da suke kamu da cututtuka masu tsanani. Kuma halayen musamman na tsarin su ne da farko dukkan mazaunan birane da gundumomi da ba su da aikin yi ciki har da tsoffi da 'yan makarantar sakandare da firamare da yara da dai sauransu suna iya shiga inshorar jiyya. Haka kuma gwamnati da fararen hula su biyu suna biyan kudaden inshorar jiyya tare, ban da wannan kuma ana iya samun kudaden inshorar jiyya ta hanyar samun gudummowar jin kai da ake bayarwa."

1 2