Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-04-28 17:12:30    
Al'adun jihar Tibet sun samu ci gaba ta hanyar cin gado da ba da kariya

cri

Abun da kuke saurara wani kashi ne daga cikin wasan kwaikwayon Tibet mai suna "Zhuowasanmu" da 'yan wasan kungiyar fasaha mai zaman kanta ta garin Reniang da ke birnin Lhasa na jihar Tibet mai ikon tafiyar da harkokin kanta ta kasar Sin suka shisshirya. Wasan kwaikwayon tibet wata irin cikakkiyar fasaha ce wadda ta zama gama gari a wuraren dake cunkushe da 'yan kabilar Tibet musamman ma a jihar Tibet, wadda kuma take bayar da labaru ta hanyar yin wake-wake da raye-waye.

Cikin 'yan shekarun nan da suka wuce, a sakamakon ci gaban da aka samu wajen tattalin arziki da zaman al'umma na jihar Tibet, jihar ta kara saurin bude kofarta ga kasashen waje, al'adu masu halayen musamman kuma masu dogon tarihi ciki har da wasan kwaikwayon Tibet suna cikin kyakkyawan yanayi, kuma an sake shisshirya wasu wasannin kwaikwayon Tibet da ke kusan bacewa. Madam Chija wata 'yar wasa ce wadda ta shafe kusan shekaru 30 tana nuna wasan kwaikwayon Tibet ta gaya wa wakilinmu cewa, "Tun lokacin da nake yarinya na fara nuna wasan kwaikwayon Tibet, a da nakan nuna wasan domin kaina, amma bayan da na shiga cikin kungiyar 'yan fasaha, mukan zabi da kuma shisshirya da nuna wasu wasannin kwaikwayon Tibet, yanzu mutane da yawa da ke zama a jiharmu ko kuma suka zo daga sauran wuraren kasar Sin da na kasashen waje, dukkansu suna son kallon wasannin da muka nuna."

Bayan da gwamnatin jihar Tibet ta tattara kuma ta shisshirya da kuma bunkasa irin wadannan al'adu masu dogon tarihi, 'yan fasaha na jihar kamar madam Chija wadanda ba ma kawai suke iya dukufa kan fasahar gargajiya da suke so ba, har ma suna samun kulawa da kariya daga wajen gamnatin jihar. Tsohuwa Samdrup, 'yar kabilar Tibet kuma wata 'yar wasannin fasaha ta jama'a ce ta jihar Tibet wadda take da shekaru 85 da haihuwa ta kware wajen nuna babban wasan kabilar Tibet mai suna "Sarkin Gesar". Domin cin gadon irin wadannan kyawawan wasanni kamar wasan "Sarkin Gesar", gwamnatin jihar ta sha gayyatar tsohuwa Samdrup zuwa jami'ar jihar Tibet da cibiyar binciken kimiyyar zaman al'umma ta jihar don ba da darasi kan fasahar nuna wasannin. A sa'i daya kuma sassan da abin ya shafa na jihar sun ba ta wurin kwana na musamman da kudin rangwame na zaman yau da kullum.

1 2