Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-04-28 17:12:30    
Al'adun jihar Tibet sun samu ci gaba ta hanyar cin gado da ba da kariya

cri

A jihar Tibet, da akwai ni'imtattun wuraren ban sha'awa na tarihi da yawa kamar fadar Potala da Norbu Lingka da wurin ibada na Sagya Monastery wadanda ke iya bayyana al'adun gargajiya da irin addinin da ake bi a wannan wuri. Mr. Xin Gaosuo, mataimakin shugaban hukumar al'adu ta jihar Tibet ya gaya wa wakilinmu cewa, "Tun bayan samun 'yancin kasa har zuwa lokacin tafiyar da shiri na l0 na shekaru 5 na raya kasa wato daga shekarar 1949 zuwa ta 2005, kasar Sin ta ware kudin Sin fiye da Yuan miliyan 500 don yin gyare-gyare da kuma kyautata kayayyakin tarihi, yanzu kuma ana tafiyar da shiri na 11 na shekaru 5 wato daga shekarar 2006 zuwa ta 2010, a cikin wannan lokacin kuma gwamnatin kasar ta tsai da kudurin cewa, za ta ware kudin Sin fiye da yuan miliyan 600 don kara yin gyare-gyare da kuma kyautata kayayyakin tarihi na jihar Tibet."

Cikin 'yan shekarun nan da suka wuce, bisa ci gaban da aka samu wajen tattalin arziki da zaman al'umma na jihar Tibet da kara bude kofarta ga kasashen waje, al'adun jihar na ta kara jawo tasiri ga kasashen duniya, baki sai kara yawa suke suna ta zuwan nan jihar domin yawon shakatawa. A sa'i daya kuma, jihar Tibet tana kara yin fadi-tashi wajen yin musanyar al'adu. Cikin 'yan shekarun nan da suka wuce kuma, jihar Tibet ta taba aike da kungiyoyi fiye da 20 zuwa kasashen ketare domin yin bukukuwan musanyar al'adu.


1 2