Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-04-28 15:55:16    
Taliban sun kai hari ga faretin sojin Afghanistan

cri

Bayan haka, a ran nan, babban sakataren MDD, Ban Ki-moon ya bayar da sanarwa, inda da kakkausan harshe ne ya la'anci al'amarin. Sanarwar ta kuma sake jaddada cewa, MDD za ta ci gaba da nuna goyon baya ga jama'ar Afghanistan da su farfado da kasarsu a karkashin jagorancin gwamnati na halal.

A ran nan kuma, babban sakataren kungiyar NATO, Jaap de Hoop Scheffer shi ma ya bayar da sanarwa, inda ya yi Allah wadai da al'amarin sosai da sosai.

Tun daga farkon shekarar da muke ciki, halin da Afghanistan ke ciki a fannin tsaro sai ci gaba da tabarbarewa yake yi, kuma hare-hare iri daban daban sun riga sun yi sanadiyyar mutuwar mutane fiye da 450. A ran 25 ga watan Maris, dakarun Taliban sun sanar da fara kai "harin bazara" kan sojojin Afghanistan da kuma sojojin kasashen waje da ke girkewa a kasar.

Don fuskantar "harin bazara" na 'yan Taliban, sojojin gwamnatin Afghanistan da sojojin kasashen waje da ke kasar sun kara karfin farautar dakarun Taliban. A ran 25 ga wata da dare a lardin Paktika da ke gabashin Afghanistan, sojojin agaji na kungiyar NATO da ke Afghanistan sun kai hare-hare kan dakarun Taliban daga sararin sama, inda a kalla dai dakarun Taliban 15 suka mutu. Don tabbatar da faretin soji da ya gudana yadda ya kamata a ran 27 ga wata kuma, gwamnatin Afghanistan ta dauki jerin matakan tsaro.

A sa'i daya kuma, a ran 25 ga wata, shugaba Karzai ya yi suka mai tsanani kan wasu ayyukan da Amurka da Birtaniya suka yi wajen yakin Afghanistan, kuma a ganinsa, kama 'yan Taliban da magoya bayansu ba shi da amfani ko kadan a wajen yaki da ta'addanci, yana fatan Amurka za ta sauya aikinta tun da wuri, kuma ta kara dora muhimmanci kan farfadowa da Afghanistan. Manazarta suna ganin cewa, wannan kyakkyawan sako ne da Mr.Karzai ya nuna wa Taliban, don neman samun goyon baya daga masu sassaucin ra'ayi da ke cikin kungiyar Taliban, ta yadda za a sassauta sabanin da ke tsakanin gwamnatin Afghanistan da Taliban. Amma duk da haka, bisa hakikanin halin da ake ciki, matakan da gwamnatin Afghanistan ta dauka bai hana harin dakarun Taliban ba. Ma iya cewa, gwamnatin Afghanistan da Taliban za su ci gaba da kiyayya da juna.(Lubabatu)


1 2