Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-04-28 15:55:16    
Taliban sun kai hari ga faretin sojin Afghanistan

cri

A jiya 27 ga wata a birnin Kabul, babban birnin kasar Afghanistan, an gudanar da faretin soji na murnar cika shekaru 16 da Afghanistan ta cimma nasarar yakar maharan Tarayyar Soviet, kuma a daidai lokacin da ake murnar wannan muhimmiyar rana, dakarun Taliban sun kai hari, wanda har ya hallaka mutane hudu, ciki har da wani dan majalisar dokokin kasar, a yayin da shugaban kasar, Hamid Karzai ya tsira da ransa.

A ran nan da safe, shugaba Karzai da dai sauran manyan shugabannin siyasa na Afghanistan sun halarci bikin da aka gudanar a birnin Kabul, kuma a lokacin da Mr.Karzai ke shirin jawabin fara bikin, sai dakarun Taliban sun harba wasu rokoki kan filin da ake gudanar da bikin, har ma sun yi musanyar wuta da sojojin gwamnati, wanda ya hallaka mutane hudu, ciki har da wani dan majalisar dokokin kasar, tare kuma da jikkata wasu mutane 7. Daga bisani kuma, kakakin dakarun Taliban, Zabiullah Mujaheed ya yi shelar daukar alhakin harin, kuma a cewarsa, dakarun Taliban 6 sun kai wannan hari ne domin shugaba Hamid Karzai, kuma an bindige uku daga cikinsu a yayin da ake musanyar wuta.

Sakamakon janye jikinsa da wuri wuri, Mr.Karzai bai ji rauni ba cikin harin. Tun bayan da Mr.Karzai ya hau kan karagar mulkin Afghanistan, kullum yana kasancewa abin bara ga 'yan Taliban, kuma kafin wannan, sau uku ne ya tsira da ransa daga kisan gillar da aka yi masa, amma wannan karo na farko ne aka kai masa hari a hedkwatar kasarsa. Daga baya, Mr.Karzai ya bayar da jawabi, inda ya yi Allah wadai da harin. Ya ce, dakarun Taliban sun kai hari a lokacin da ake bikin murnar cika shekaru 16 da Afghanistan ta cimma nasarar yakar maharan Tarayyar Soviet, lallai sun lalata muhimmin biki na kasar Afghanistan da na jama'arta. An ce, Mr.Karzai ya riga ya umurci a bi bahasin al'amarin, kuma a halin yanzu, sojojin tsaron Afghanistan sun kama mutane da dama da ake tuhumarsu da sa hannu cikin harin.

1 2