Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-04-25 15:27:31    
Aikin share fagen wasan sukuwar dawaki na gasar wasannin Olympics na Beijing na gudana lami-lafiya

cri

A lokaci guda, Mr. Henry Tang ya fadi cewa, mambobin kwamitocin wasannin Olympics na kasashe da yankuna masu tarin yawa sun taba kawo ziyarar duba aiki a gine-gine da filayen da abin ya shafa, inda dukkaninsu suka gamsu sosai da ganin kyawawan gine-gine da shirye-shirye na Hongkong. A karshe dai, Mr. Henry Tang ya yi takaitaccen bayanin cewa: " Kimanin watanni hudu ke nan da suka yi saura a gudanar da gasar sukuwar dawaki ta wasannin Olympics. Bisa wannan yanayi dai, kwamitin kula da harkokin wasan dawaki na Hongkong zai gaggauta bada horo a fannin zirga-zirga, da tsaro, da takaita yawan tafiye-tafiyen mutane, da aikin binciken cututtukan dabbobi da kuma ma'aikatan sa kai, ta yadda za a bada tabbaci daga dukkan fannoni ga ayyukan share fage domin marhabin da zuwan gasannin Olympics".

Hadaddiyar kungiyar kula da harkokin wasan dawaki ta kasa da kasa ta yi zamanta a birnin Lausanne na kasar Swiss,wanda ya samu halarar wakilai 160 daga kasashe 25 na duniya, wadanda daukacinsu suka buga take ga ayyukan share fagen da gwamnatin yankin Hongkong take yi.( Sani Wang )


1 2