Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-04-25 15:27:31    
Aikin share fagen wasan sukuwar dawaki na gasar wasannin Olympics na Beijing na gudana lami-lafiya

cri

Aminai 'yan Afrika, ko kuna sane da cewa, bisa shirin da aka tsara an ce, za a gudanar da wasan sukuwar dawaki na gasar wasannin Olympics ta Beijing a yankin Hongkong na kasar Sin. Kuma aikin share fagen gasar sukuwar dawaki ta wasannin Olympics na Beijing har kullum yakan janyo hankulan mutane. Mr. Henry Tang, shugaban kwamitin kula da harkokin sukuwar dawaki na kwamitin shirya gasar wasannin Olympics ta 29 kuma shugaban sashen kula da harkokin gwamnati na yankin Hongkong na kasar Sin da kuma sauran mambobin kwamitin kula da harkokin sukuwar dawaki na Hongkong sun yi aikin rangadi kwanan baya bada dadewa ba a kauyen 'yan wasa da kuma 'yan wasa nakasassu, da muhimman filayen gasar sukuwar dawaki na wasannin Olympics dake unguwar Sha Tin ta yankin Hongkong domin samun labari dangane da ci gaban aikin gina gine-gine na filin wasan sukuwa, inda Mr. Henry Tang ya furta cewa, aikin share fagen gasar sukuwar dawaki ta wasannin Olympics na Beijing na gudana lami-lafiya. Bayan aikin rangadin, Mr. Henry Tang ya furta cewa: "Ina farin ciki matuka da ganin yadda ake gudanar da aikin share fagen kauyen 'yan wasa na Olympics kamar yadda ya kamata. Lallai an kaddamar da cikakken shiri a fannin gidajen kwana, da abinci da kuma na tsaro da dai sauran fannoni, musamman ma an harhada dakin kwana irin na musamman domin 'yan wasa nakasassu na sukuwar dawaki, wadanda sukan yi amfani da kujeru masu taya".

Ko kuna sane da cewa, a cikin tarihin gasar wasannin Olympics da aka gudanar a da, sau daya ne kawai aka taba ganin cewa filin gasar wasa daya tilo na da tazarar kilo-mita sama da 1,000 daga birni mai masaukin gasar wasannin Olympics da aka gudunar a Melbourne na kasar Australiya a shekarar 1950. Saboda dalilin dudduba ingancin dabbobi ne, aka yanke shawarar gudanar da gasar sukuwar dawaki a kasar Sweden. Bisa wannan dalili ne, a watan Yuli na shekarar 2005, kwamitin wasannin Olympics na kasa da kasa ya tsaida kudurin mayarda yankin Hongkong na kasar Sin a matsayin wurin gudanar da gasar sukuwar dawaki ta wasannin Olympics na Beijing.

A kolejin wasannin motsa jiki na Hongkong a unguwar Sha Tin, mambobin sun kuma duba nau'rorin sanyaya dakunan dawaki, da ayyukan hidima ga dabbobi da kuma filin horo na cikin daki, inda aka girke na'u'o'in iyakwandishan. Mr. Henry Tang ya yi yabo da cewa: " Lallai ingancin na'urori iri daban-daban da aka harhada a cikin dakunan dawakin ya kai labari, wadanda kuma ka iya bada tabbaci ga samun kyakkyawan tsaro na dawaki masu shiga gasa a duk lokacin da suke zama a Hongkong".


1 2