Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-04-23 20:09:33    
Wani bikin da ke cikin bukukuwa 24 na yanayin sararin samaniya na kasar Sin, wato ranar bikin ruwan sama

cri

A zamani aru aru na kasar Sin, da akwai wata maganar da cewa, ruwan sama na yanayin bazara yana da daraja sosai tamkar yadda darajar mai take yi, a wajen zaman rayuwar manoman da ke dogara da sha'anin noma, ruwan sama da aka yi a farkon lokacin zuwan yanayin bazara, na da amfani sosai ga manoma. Bisa abubuwan da aka tanada a cikin bayanan tarihi dangane da sararin samaniya , an bayyana cewa, a ranar bikin ruwan sama, ana ruwan sama a yawancin wuraren kasar Sin, in ana ruwa a wannan rana, to zai ba da tasiri mai muhimmanci ga ayyukan noma. A cikin jama'a, game da karin magana dangane da bikin ruwan sama na da yawan gaske wadanda suka bayyana kaunar manoma a kan ruwan sama. Alal misali, "ana ruwa a ranar bikin ruwan sama, tsire-tsiren gona za su girma sosai, a ko'ina ana samun abubuwa masu daraja sosai a yanayin bazara" ma'anar karin magana ita ce haka, a ranar bikin ruwan sama, in ana ruwan sama, to tsire-tsiren gona za su girma sosai, in tisre-tsiren gona suna kamawa sosai, to manoma za su sami kaka mai armashi. "ranar bikin ruwan sama tana kusanci, yanayin sararin samaniya yana kara dumi, kuma ana jigilar taki zuwa gonaki kai da kawowa", wato ana ganin cewa, a lokacin bikin ruwan sama, yanayin sararin samaniya yana kara dumi, lokacin nan lokaci ne mai muhimmanci da tsire-tsiren gona ke kamawa sosai, daga wannan lokaci, wasu tsire-tsiren gona da aka shuke su a yanayin hunturu su ma suna bukatar ruwa da yawa , ya kamata a yi musu taki a daidai lokacin da suke bukata da jan ruwa gare su. A cikin jama'ar kasar Sin, ana ganin cewa, in ana ruwa a wannan rana, to za a yi ruwan sama a duk shekarar a daidai yadda ya kamata.

Amma dayake kasar Sin tana da makekiyyar kasa, yanayin sararin samani na kudu da na arewa na da bambanci sosai. A wuraren kudancin kasar Sin, kamar su lardin Kwandong da Hainan da Kwanxi da sauran larduna da jihohi, ba a sami sanyi sosai a yanayin hunturu, ana kuma kan samun ruwan sama, amma a arewancin kasar Sin, kamar su Mongoliya ta gida da Helongjiang da sauran larduna da jihohi, ana kankara mai taushi bayan lokacin zuwan ranar bikin ruwan sama. A takaice dai, bayan ranar bikin ruwan sama, yanayin sararin samaniya ya kara dumi, kuma ana kara ruwan sama da yawa. Dukan wadannan bayanai su ne sakamakon da jama'ar Sin suka samu a cikin darurukan shekaru, kuma suna da bayanin shadawa daga wajen kimiyya, za su iya ba da jagoranci ga manoma wajen aikin noma da zaman rayuwarsu.(Halima)


1 2