A cikin shirinmu na yau, za mu yi bayani kan ranakun bukukuwan yanayin sararin samaniya na kasar Sin. Game da ranar bikin yanayin sararin samaniya, an bayyana cewa, bisa sauyawar yanayin sararin samaniya da yawan ruwan sama da ake samu da tsawon lokacin saukar jaura da dai sauran almomin halittu ne, aka raba shekara guda don ta zama matakan lokutan bayyana almomin yanayin sararin samaniya lokaci lokaci, ranakun bukukuwan yanayin sararin samaniya su ne ranakun somawar wadannan matakan lokutan bayyana almomin yanayin sararin samaniya. Tsara tsarin ranakun bukukuwan yanayin sararin samaniya shi ne sakamakon da jama'ar zamani aru aru na kasar Sin suka samu a lokacin da suke duddubawa tare da yin nazari kan ilmin yanayin sararin samaniya . Wannan yana da tasiri mai muhimmanci sosai ga harkokin noma. Bisa bayanan da aka tanada, an rubuta cewa, a shekarar 104 kafin bayyanuwar Annabi Isa (A.S), mutanen kasar Sin sun riga sun tsara tsarin ranakun bukukuwan yanayin sararin samaniya, don tunawa da su sosai, mutanen zamanin da sun kuma tsara wakoki dangane da ranakun bukukuwan yanayin sararin samaniya.
Bikin ruwan sama shi ne biki na biyu da ke cikin bukukuwa 24 na yanayin sararin samaniya bayan bikin wani matakin yanayin sararin samaniya na kasar Sin, wato ranar bikin somawar yanayin bazara. A kowace shekara , a ranar 18 ko ranar 19 ko ranar 20 ga watan Fabrairu, wani biki ne da ya zo don bayyana halin da halittu ke ciki na saukar ruwan sama.
A cikin littafin tanadin layin rana da wata da shekara na zamani aru aru na kasar Sin , an rubuta cewa, "iskar da ta tashi daga gabashin duniya ta narke kankara, kuma kankara da kankara mai taushi sun bace sun zama ruwan sama". A wuraren da ke dab da kogin rawayen kogi, wato a wuraren da ke nuna asalin bukukuwa 24 na yanayin sararin samaniya, lokacin zuwa bikin nan ya bayyana cewa, ana kara damshi sosai a cikin iska, kuma ana kara samun ruwan sama da kuma ana kara samun dumi a arewacin kasar Sin. Kuma ya bayyana cewa, yanayin hunturu mai sanyi sosai tare da saukar kankara mai tashi da yawa zai wuce, kuma ranakun samun damshi da rana mai dumi da ruwan sama sai kara yawa suke yi, mutane sun ji cewa, yanayin bazara yana tafiya yana zuwa yana kusancinmu, kuma furanni suna soma budewa.
1 2
|