Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-04-22 16:26:48    
Wurin yawon shakatawa na gandun daji na Paotaiwan da ke wuri mai danshi

cri

An yi karin bayanin cewa, in an kwatanta shi da sauran wuraren yawon shakatawa iri daban daban fiye da 100 a birnin Shanghai, wurin yawon shakatawa na gandun daji na Paotaiwan yana da albarkatun al'adun mutane masu siggogin musamman. Yana bakin kogin Yangtse da kogin Huangpujiang a gabas, yana dab da babban tsaunin Paitaishan a yamma, a kusurwarsa a kudu maso yamma, akwai muhimmin wuri a harkokin aikin soja wato Wusongkou. A zamanin daular Qing, mahukuntan zamanin daular Qing sun gina wurin harba manyan bindigogin igwa saboda wannan wuri na da muhimmanci sosai a harkokin aikin soja. Wani shahararren janar na zamanin daular Qing ya taba jagorantar sojojinsa domin yaki da sojoji mahara na kasar Birtaniya, ya kuma rasa rayukansa a nan. Kazalika kuma, a karshen zamanin daular Qing, kasar Sin ta soma shimfida hanyar dogo ta farko wato hanyar dogo ta Songhu daga nan zuwa Zhabei na birnin Shanghai. A farkon lokacin da kasar Sin take yaki da sojojin mahara Japanawa, sojojin kasar Sin sun taba yin musayar wuta mai tsanani tare da sojojin Japan, sun sami nasarar hana mahara Japanawa su sauka Paotaiwan.

Domin kiyaye wurin yawon shakatawa na gandun daji na Paotaiwan da ke wuri mai danshi, wanda ya fi girma a birnin Shanghai, haka kuma shi ne na farko a wannan birni, mazauna wurin sun kafa kungiyar masu aikin sa kai da ke kunshe da mutane dari daya, suna bai wa masu yawon shakatawa hidimomi a wannan wurin yawon shakatawa mai kyaun gani.(Tasallah)


1 2