Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-04-22 16:26:48    
Wurin yawon shakatawa na gandun daji na Paotaiwan da ke wuri mai danshi

cri

A shekarar bara, an bude wurin yawon shakatawa na gandun daji na Paotaiwan, wanda ya fi girma a birnin Shanghai da ke gabashin kasar Sin a matsayin wurin yawon shakatawa na gandun daji da ke wuri mai danshi. An gina shi ne a kusa da wani muhimmin wuri a harkokin aikin soja wato Wusongkou kuma a bakin kogin Yangtse.

Wurin yawon shakatawa na gandun daji na Paotaiwan yana kasancewa a wurin da kogin Yangtse da kogin Huangpujiang suka hadu da juna, fadin wuri mai danshi a cikinsa ya wuce kadada 50. Ana iya ganin kyan karkara na halitta na bakin kogin Yangtse da kuma dubban dogayen itatuwa da ciyayi masu tsawo a wannan wurin yawon shakatawa. Ban da wannan kuma, a bakin kogin, an hada wasu tsibirai manya da kanana gaba daya, a ko wace rana da safe da kuma yamma, ana iya ganin kyan karkara irin ta musamman a wuri mai danshi mai fadin murabba'in mita dubu dari 1 ko fiye a sakamakon sauye-sauyen zurfin ruwa. A gun wadannan tsibirai, masu yawon shakatawa suna iya ganin kyan karkara irin na kwaruruwa da na hamada da kuma na wurare masu danshi da ke bakin kogi ko bakin teku, sa'an nan kuma, suna iya yin wasa da na'urorin nishadi a harkokin aikin soja, saboda a can da, wurin da aka gina wannan wurin yawon shakatawa, wuri ne da aka gina wani muhimmin sansani na rundunar sojojin jiragen ruwa.


1 2