Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-04-22 16:25:03    
Lhasa na neman raya kanta zuwa birni tamkar wurin yawon shakatawa na matsayin kasar

cri

An ce, Lhasa ta tsara tunanin kafa birni tamkar wurin yawon shakatawa na halittu, wato fito da tsarin hada al'adun tarihi da dasa ciyayi gaba daya da kuma raya birni da kauyuka tare, sa'an nan kuma, za ta kara dasa ciyayi da kara ire-iren ciyayi, ta haka za ta hada tsarin filayen ciyayi da tsarin ruwa da kuma al'adun tarihi tare. Bugu da kari kuma, za ta dora muhimmanci kan kara fadin filayen ciyayi a bankuna 2 na kogin Lhasa, ban da wannan kuma, za ta mai da hankali kan kara fadin filayen ciyayi a bankuna 2 na kogunan Zhongganqu da Liushanhe da Duilongqumahe. Za ta kuma hada gidan ibada na Jokhang da fadar Potala da wurin yawon shakatawa na Norbulingka da hanyoyin dogo da hanyoyin mota.

Kazalika kuma, Lhasa za ta kara yawan wuraren yawon shakatawa da fadin filayen ciyayi a tsohon bangare da sabon bangare nata, ta haka Lhasa za ta zama birnin da ya yi kamar wurin yawon shakatawa na halitta, kuma ya iya nuna kyakkyawar sigar musamman na kananan kabilu.(Tasallah)


1 2