Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-04-22 16:25:03    
Lhasa na neman raya kanta zuwa birni tamkar wurin yawon shakatawa na matsayin kasar

cri

Don kyautata siffarta da inganta karfinta na takara daga dukan fannoni da kuma kayatar da birnin, birnin Lhasa ya kaddamar da aikin kafa birni tamkar wurin yawon shakatawa na muhallin halittu a matakin kasar a shekarar 2007, yana rubanya kokarinsa domin cimma burinsa a shekarar 2012. A lokacin, fadin wurare a cikin birnin da aka dasa ciyayi da itatuwa zai kai kadada 2500 ko fiye, sa'an nan kuma, yawan wuraren da aka dasa ciyayi da itatuwa zai wuce kashi 45 cikin dari bisa jimlar fadin birnin, haka kuma, yawan wuraren da aka dasa ciyayi zai wuce kashi 38 cikin dari bisa jimlar fadin birnin.

Birnin da ya yi tamkar wurin yawon shakatawa irin na muhallin halittu, wani irin birni ne da aka hada sigar musamman ta wurin yawon shakatawa da ta birni sosai. Sigogin musamman na irin wannan birni su ne akwai ni'itattun wurare a cikin birni, haka kuma, birnin na kasancewar tamkar cikin wani wurin yawon shakatawa mai kyaun gani. Ban da wannan kuma, muhalli ya yi kyau a birnin, ana iya ganin sararin samaniya mai launin shudi da ruwa mai tsabta da kuma wuraren ciyayi a ko ina a wurin.

Bisa kididdigar da aka yi, an ce, ya zuwa yanzu dai, fadin wurare a Lhasa da aka dasa ciyayi ya kai misalin 1700 ko fiye, yawan wuraren da aka dasa ciyayi da itatuwa ya kai kashi 30.36 cikin dari bisa jimlar fadin Lhasa, yawan wuraren ciyayi ya kai kashi 30.27 cikin dari bisa jimlar fadin birnin, matsakaicin fadin wuraren ciyayi da ko wane mutum ke mallaka zai kai murabba'in mita 23.07. Bugu da kari kuma, Lhasa ta yi fintikau a fannonin ingancin iska da dasa gandun daji, ta haka ta aza harsashi mai kyau wajen neman kafa birni tamkar wurin yawon shakatawa na halittu.


1 2