Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-04-21 14:57:22    
Mr. Gao Yunliang, dan kabilar Yi da iyalinsa

cri

Iyalin Gao Jinfeng wani babban iyali ne a wannan wuri, da akwai mutane kusan 20 a gidansa, ban da 'ya'ya 3 na kansa, kuma yana ciyar da yara marayu 6 da ya samu daga danginsa. A da babu lambun itatuwa masu ba da 'ya'ya a gidansa, suna tafiyar da zama ne ta hanyar aikin gona kawai. Daga baya kuma matarsa mai suna Ji Meilian ta koya fasahar kiwon aladai daga wajen mutane 'yan kabilar Han, kuma tana kiwon wasu aladu a gidansa, wannan ya zama wata hanya daban da suke bi domin samun kudin shiga. Yanzu dukkan 'ya'yanta sun yi girma kuma suna ba da taimako gare ta, shi ya sa yanzu ta fara jin dadi. Ta ce,

"A da babu surukuwa a gidana, nakan tashi daga barci tun da sassafe wato tun karfe 4 da safe, bayan na tashi sai na dafa abinci, daga baya kuma na ciyar da aladu da yin aikin gona. Amma yanzu da akwai mutanen da suke ba ni taimako, shi ya sa nakan zauna a gida tare da jikokina."

A shekarar 2007, madam Ji Meilian ta ci zaben zama mutuniya mai ba da misali ta lardin Hainan na kasar Sin sabo da ta nuna kyawawan halayen da'a wajen ciyar da marayu da girmamawa iyayenta.(Umaru)


1 2 3