Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-04-21 14:57:22    
Mr. Gao Yunliang, dan kabilar Yi da iyalinsa

cri

Cikin shirinmu na yau, za mu kawo muku wani bayani kan kabilar Yi, kabilar da ke lardin Hainan na kasar Sin tun shekara da shekaru. Kabilar Yi tana daya daga cikin kabilu mafiya dogon tarihi a kudancin kasar Sin, 'yan kabilar Yi suna zama a tsibirin Hainan tun kakanni-kakanninsu, yawan 'yan kabilar da ake da su yanzu ya wuce miliyan 1.3. Gundumar Baoting ta kabilar Yi da ta Miao mai ikon tafiyar da harkokin kanta da ke kudu maso gabashin lardin Hainan tana daya daga cikin wuraren da suke cunkushe da mutane 'yan kabilar Yi.

In ka dau mota daga birnin Haikou, hedkwatar lardin Hainan, ka bi hanyar mota ta gabashin lardin cikin awa 4, sai ka isa gundumar Baoting. A nan da akwai itatuwa da yawa, kuma da yanayi mai dadi, daga cikin mutane dubu 160 na duk gundumar, yawan mutane 'yan kabilar Yi kuma ya kai kusan dubu 100. Mr. Gao Yunliang wanda yake da shekaru 76 da haihuwa yana zama a kauyen Tongzha na garin Jiamao da ke gundumar Baoting tun kakanni-kakanninsa, shi ne shahararren magini, tun lokacin da yake saurayi ya fara aikin gina bukkokin gargajiya na kabilar Yi wadanda siffarsu ta yi kamar kwalekwale.

Yanzu Mr. Gao da 'ya'yansa sun riga sun yi kaura daga irin wannan bukka zuwa wani babban daki mai hawa 2 wanda fadinsa ya kai fiye da murabba'in mita 300.

"A lokacin da nake saurayi, ni wani injiniya ne mai gina bukkoki, ba na je yawo a kullum ba, nakan taimaka wa manoman kauyenmu wajen gina bukkoki masu siffar kwalekwale na kabilar Yi, amma ban iya yin fasali da gina gidaje da karafa da sumunti ba. Yanzu na riga na tsofu, na yi aikin noma kadan, 'ya'yana sun samu kudi sun gina wannan babban gida mai haske kuma mai dadin barci."


1 2 3