Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-04-18 13:45:27    
Sakonnin masu sauraro kan wasannin Olympics na Beijing

cri

Kan maganar kallo kuwa, ai ni ina matukar son tseren dawaki, domin ya na matukar burge ni, ka san mutumin Bauchi da son dawaki, kuma duk lokacin da za'a a gwada wannan wasa zan gani da yardar Allah."

To, muna godiya ga dukan masu sauraro da suka rubuto mana, ciki har da wadanda ba mu karanta wasikunsu ba, sabo da karancin lokaci, muna kuma godiya ga goyon bayan da suka nuna wa wasannin Olympics na Beijing. Kamar yadda masu sauraronmu suka fada, wasannin Olympics dandali ne na sada zumunta a tsakanin al'ummar duniya baki daya, kuma duk wanda ke kaunar zaman lafiya da gaskiya, ba shakka zai rungume shi. Abin da za mu ce kawai shi ne, sai mu hadu a dandalin a watan Agusta mai zuwa.

Sa'an nan, ga wasu tambayoyi daga hannun shugaba Mohammed Idi Gargajiga, Gombawa kungiyar masu sauraren gidan rediyon CRI, jihar Gombe, tarayyar Nijeriya. A cikin wasikar da malamin ya aiko mana kwanan baya, ya sanya mana wasu tambayoyin da yake so mu ba shi cikakken bayani mai gamsarwa. Tambayoyinsa su ne "a lokacin da za a gudanar da gasar wasannin Olympics ta Beijing a shekarar 2008 da muke ciki, ko gidan rediyon kasar Sin zai sa hannu adama da shi domin kawowa masu sauraronsa bayanai kan gasar? Harsuna nawa ne gidan rediyon kasar Sin zai kebe domin shirye-shiryen musamman na gasar wasannin Olympics ta Beijing? Kuma daga wane lokaci ne CRI zai soma watsa shirye-shirye na musamman kan gasar wasannin Olympics na Beijing? Daga cikin kayayyakin wasannin da za a yi amfani da su a lokacin gasar wasannin Olympic ta Beijing, shin ko akwai kayayyaki na kasar Sin wadda ta kera ko ta yi su daga ciki?"

To, madallah, malam Mohammed Idi Gargajiga, mun gode da ka turo mana tambayoyin. Ba shakka a lokacin wasannin Olympics na Beijing, gidan rediyon kasar Sin zai taka muhimmiyar rawa wajen kawo wa masu sauraronsa rahotanni masu gamsarwa kan gasar, kuma dukan sassansa, wato sassan harsunan waje 38, ciki kuwa har da sashen Hausa, da sassan yaren Sinanci 5, za su kebe shirye-shiryen musamman domin gasar, kuma a hakika, ba ma kawai a lokacin gasar ba, tun tuni, mun fara gabatar da shirye-shirye game da wasannin Olympics da za a gudanar a nan Beijing, ciki har da rahotanninmu na musamman a kowace rana game da bikin mika wutar wasannin Olympics da ake yi a kasashe daban daban, da kuma shirinmu na "Beijing a shekarar 2008" da muke gabatar muku a duk ranakun Laraba da Jumma'a. Muna fatan da shugaba Mohammed da kuma sauran masu sauraronmu za ku kasance tare da mu a cikin shirin, domin ku sami cikakken bayani game da wasannin Olympics da za a gudanar a nan birnin Beijing.

Sa'an nan, a game da ko akwai kayayyakin wasanni da Sin ta kera wadanda za a yi amfani da su a lokacin wasannin Olympics, I, haka ne, a hakika dai, masana'antun kasar Sin da ke da tambarinsu na kansu za su samar da kayayyakin wasanni ga manyan wasanni 14 daga cikin 26 da za a gudanar, kuma ba sabo da Sin ta karbi bakuncin gudanar da wasannin Olympics ba, shi ya sa masana'antunta suna iya samar da kayayyakin wasanni, a'a, ba haka ba ne. A fannin zaben kayayyakin wasannin da za a yi amfani da su a gun wasannin Olympics, hukumar kula da wasannin Olympics ta duniya da kungiyoyin wasa iri iri na duniya suna da ka'idoji masu tsanani, kuma ko kadan ba za su nuna fifiko ga kasar da ke daukar nauyin gudanar da wasan ba, kuma dalilin da ya sa masana'antun Sin suka iya samar da kayayyakin wasanni ga dimbin wasannin shi ne, sabo da kokarin da suka shafe shekara da shekaru suka yi, kuma duk wani kayan wasan da ya cancanta a yi amfani da shi ya ci jarrabawar manyan gasannin duniya iri iri.(Lubabatu)


1 2