Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-04-18 13:45:27    
Sakonnin masu sauraro kan wasannin Olympics na Beijing

cri

Jama'a masu sauraro, assalamu alaikum, barkanku da war haka, barkanmu kuma da saduwa da ku a zaurenmu na "amsoshin wasikunku", kuma ni ce Lubabatu ke gabatar muku da wannan shiri a duk ranakun Jumma'a daga nan sashen Hausa na rediyon kasar Sin.

Masu sauraro, nan gaba ba da jimawa ba, Sin za ta fara gudanar da wasannin Olympics, kuma yanzu tana share fage sosai ga wasan. Ba shakka wasannin Olympics wani kasaitaccen biki ne na al'ummar duniya baki daya, kuma yana jawo hankulan jama'a sosai, kuma masu sauraronmu ma suna mai da hankulansu sosai a kan wasan, har ma sun sha rubuto mana ra'ayoyinsu kan wasan.

Malam Yakubu Sanusi daga garin Duna, karamar hukumar Kamba, jihar Kebbi, tarayyar Nijeriya, ya rubuto mana cewa, "Gasar wasan Olympic yana da muhinmanci kwarai da gaske, kuma yana sada zumunta tsakanin kasashen da suke cikin wasan. Abin farin ciki shi ne yadda wasan Olympic ya yi suna da kuma yin fice fiye da yadda sauran wasanni ke tasiri, abin ban sha'awa shi ne Gidan Radion kasar Sin, wato China radio international tana taimakawa masu sauraro domin sanin yadda kasar sin take gudanar da wannan wasan."

Sai kuma malam Salisu Muhammed Dawanau, mazaunin birnin Abuja, tarayyar Nijeriya, ya rubuto mana wasikar cewa, " Gasar wasannin Olympic na bana, wadda za'a yi a kasar Sin, mai taken "Duniya daya, mafarki daya", hakika Olympic ce mai alamar haske wacce za ta nuna wa duniya kasar Sin da al'ummarta da kuma al'adun kasar mai tsawon tarihi da kuma muhimmanci.

Fata na a koda yaushe, tun lokacin da kasar Sin ta samu damar daukar nauyin wannan gasa ta olympic, shi ne "Allah Ya kai mu watan Agusta ta wannan shekara domin a gudanar da wannan gasar cikin kwanciyar hankali da cin nasara. Kuma ya kasance duk kasashen da za su halarta su samu jin dadi a yayin da ake olympic din."

Kwanan nan, watakila ku masu sauraronmu kun sami labarin cewa, akwai wadanda ke yunkurin kawo cikas ga wasannin Olympics da za a gudanar a kasar Sin. A dangane da batun, kwanan baya, malam Babangida Adamu, daga birnin Bauchi, tarayyar Nijeriya, ya rubuto mana ra'ayinsa cewa, "ra'ayina kan wassannin Olympic da za a yi a birnin Beijin shi ne, ina mai fatan a fara lafiya kuma a gama lafiya, domin yadda nake sauraro a kafofin watsa labarai, sai abin yana nuna mun kamar yammacin duniya na son sa siyasa a cikin abin, domin gasar ya samu chikas, amma na yi tunanin cewa, wannan ba wani abin mamaki ba ne, domin duk lokacin da za'ayi wani abu wanda suka ga alamar akwai nasara ciki kuma ba daga wurin su ya fito ba, to sai su yi ta kokarin kawo cikas cikin al'amuran, yanzu misali mai ya hada maganar Tibet da wassannin olympic, amma suna ta kokarin sai sun hada maganan wuri daya domin cimma wassu manufofinsu na daban.


1 2