Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-04-16 17:36:52    
An yi taron tattaunawa a tsakanin Sin da Birtaniya kan harkokin tattalin arziki da kudi a karo na farko

cri

Makasudin kafa tsarin yin taron tattaunawa a tsakanin Sin da Birtaniya kan harkokin tattalin arziki da kudi shi ne domin daukaka yin hadin gwiwa a tsakanin Sin da Birtaniya a harkokin tattalin arziki da kudi da kuma kara tuntubar juna a tsakanin kasashen 2 a manyan batutuwan kudi na duniya da kara samun ra'ayi daya da kuma inganta da zurfafa dangantakar abokantaka a tsakaninsu bisa manyan tsare-tsare daga dukkan fannoni. A farkon wannan shekara, a lokacin da yake yin ziyara a kasar Sin, firayim ministan Birtaniya Gordon Brown da takwaransa na kasar Sin Wen Jiabao sun sami ra'ayi daya sun kuma yarda da yin taron tattaunawa kan harkokin tattalin arziki da kudi a tsakanin mataimakan firayim ministoci na kasashen 2, a maimakon a tsakanin mataimakan ministocinsu a da.

A gun taron tattaunawar da aka yi a ran 15 ga wata, bangarorin Sin da Birtaniya sun sami ra'ayi daya a fannoni da yawa. Birtaniya ta yi alkawarin ci gaba da sa kaimi kan kungiyar tarayyar Turai da ta amince da cikakken matsayin kasuwanci na kasar Sin cikin sauri. A gun taron manema labaru cikin hadin gwiwa, Mr. Darling ya ce,'Mun yi taron tattaunawar ne bisa wani irin ra'ayi daya, wato budaddiyar kasuwa da kuma yin ciniki ba tare da shinge ba sun fi nuna muhimmanci wajen samun wadatuwar tattalin arziki, su ne kuma abubuwan da suka wajaba wajen raya tattalin arziki mai dorewa. Dukkanmu na ganin cewa, ya kamata a taka rawa mai yakini, a himmantu wajen kafa budadden tsarin zuba jari a fili.'

Game da ra'ayi daya da Sin da Birtaniya suka samu a wannan karo, Mr. Wang yana ganin cewa, wannan ya nuna cewa, Sin da Birtaniya za su iya kawar da bambanci a tsakaninsu, kuma za su iya daukaka amincewa da juna bisa manyan tsare-tsare domin tabbatar da yin hadin gwiwar moriyar juna. Ya ce,'Samun nasarar kaddamar da taron tattaunawar da kuma samun ra'ayi daya a fannoni da yawa sun nuna cewa, kasashen Sin da Birtaniya za su iya kawar da bambanci a tsakaninsu a fannonin tarihi da al'adun gargajiya da tsarin zaman al'ummar kasa da matsayin bunaksuwar tattalin arziki da zaman al'ummar kasa, ta haka sun iya daukaka amincewa da juna bisa manyan tsare-tsare da kuma tabbatar da yin hadin gwiwa domin moriyar juna. Na yi imani da cewa, a cikin sabon halin da muke ciki, kokarin da Sin da Birtaniya suke yi domin neman samun sabbin hanyoyi da fannonin da za su iya hadin gwiwa a kai a harkokin tattalin arziki da kudi zai ba da babban taimako wajen zurfafa dangantakar abokantaka a tsakaninsu bisa manyan tsare-tsare.'(Tasallah)


1 2