Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-04-16 17:36:52    
An yi taron tattaunawa a tsakanin Sin da Birtaniya kan harkokin tattalin arziki da kudi a karo na farko

cri

Ran 15 ga wata, a nan Beijing, an yi taron tattaunawa a tsakanin kasashen Sin da Birtaniya kan harkokin tattalin arziki da kudi a karo na farko. Wang Qishang, wakilin musamman na firayim ministan kasar Sin kuma mataimakin firayim ministan kasar da Alistair Darling, wakilin musamman na firayim ministan Birtaniya kuma ministan kudi na kasar sun halarci taron tare da jami'an kasashen 2 da ke kula da tattalin arziki da kudi da ciniki da harkokin waje.

Bayan taron, Mr. Wang da Mr. Darling sun gana da manema labaru na gida da na waje cikin hadin gwiwa. Mr. Wang ya ce,'Bisa babban take na 'yin hadin gwiwa a tsakanin Sin da Birtaniya a fannonin tattalin arziki da kudi', cikin sahihanci kuma ba tare da boye abubuwa ba ne bangarorin 2 muka yi mu'amala kan raya tattalin arzikinmu mai dorewa da yin hadin gwiwar ba da hidimar kudi da kuma daidaita dama da kalubalen da bunkasa tattalin arzikin duniya gu daya ke kawowa. Shirya taron tattaunawar ya almantar da cewa, ra'ayi daya da firyaim ministocin kasashen 2 suka samu, wato yin taron tattaunawa a tsakanin mataimakan firayim ministoci na Sin da Birtaniya kan tattalin arziki da kudi, ya zama abin gaskiya, haka kuma taron ya ba da taimako wajen habaka hadin gwiwar tattalin arziki a tsakanin Sin da Birtaniya daga dukkan fannoni, da kuma daukaka ci gaban dangantakar abokantaka a tsakanin kasashen 2 bisa manyan tsare-tsare daga dukkan fannoni.'


1 2