A halin da ake ciki yanzu, an riga an mayar da wasannin motsa jiki a matsayin ma'aunin nuna bunkasuwar lafiyar jiki da wayin kai na dan adam, wato babu nasaba tsakaninsu da duhun kai, amma a gun gasar wasannin Olympic ta zamanin da, wasu 'yan wasa sun rasa rayuka a cikin wasan. Wanda ya fi tsanani shi ne wasan dambe. A cikin shirinmu na yau, bari mu kawo muku bayani kan wannan.
A gun gasar wasannin Olympic na zamanin da, wasan dambe shi ma ya sami karbuwa sosai a tsohuwar kasar Greece, kuma jama'ar tsohuwar kasar Greece suna mayar da 'yan wasan dambe mafiya nagarta a matsayin gumaka. A gun zama na 23 na gasar wasannin Olympic na zamanin da da aka yi a shekarar 688 kafin haihuwar Annabi Isa alaihissalam, aka fara yin gasar wasan dambe.
Da farko dai, 'yan wasan dambe suna sa safar hannu irin ta fatar sa mai laushi, wato an sa fatar sa cikin mai, daga baya kuma fatar za ta zama mai laushi. Tun daga karnin 5 kafin haihuwar Annabi Isa alaihissalam, aka fara yin amfani da safar hannu iri ta fatar sa mai tauri. Ya zuwa zamanin Roma, wato wajen karnin 2 kafin haihuwar Annabi Isa Alaihissalam safar hannu ta wasan dambe ta canja, an sa karfe mai kaifi a kanta, a sanadiyar haka, 'yan wasa su kan ji rauni mai tsanani, ana iya cewa, wasan dambe na gasar wasannin Olympic ta zamanin da wasa ne mai hadari, kuma shi ne wasa mai zuba jini. 'Yan wasa sun yi gasa ta hanyar yin canki-canki, wanda ya rasa nasara, sai ya daga hannun dama, ya bar filin gasa, a karshe dai, wanda ya zama na karshe a filin gasa shi ne zakara.
1 2
|