Bugu da kari kuma, baya ga Sinanci da harshen kabilar Tibet da Turanci, wasu ma'aikatan da ke aiki a cikin kantuna a birnin Lhasa sun iya harsunan Indiya da Nepal.
Yanzu saboda karuwar yawan masu yawon shakatawa na kasashen waje, rukunin yawon shakatawa na jihar Tibet ya kara mai da hankali kan yin mu'amala cikin harsuna daban daban. A cikin yawancin sana'o'i, ma'aikata suna iya ba da hidima cikin Sinanci da Turanci da harshen kabilar Tibet. Sa'an nan kuma, a ko ina ana iya samun takardun sunayen abinci da takardun bayani cikin Sinanci da Turanci da harshen kabilar Tibet.
A cikin dakunan ajiye kayayyakin tarihi a jihar Tibet, masu jagora suna iya yi wa masu yawon shakatawa na gida da na waje bayani cikin Sinanci da Turanci da Jamusanci da Japananci da kuma harshen kabilar Tibet, ana kuma samar da injunan yin bayani cikin Sinanci da Turanci da Japananci da kuma harshen kabilar Tibet. A sauran shahararrun wuraren yawon shakatawa a jihar Tibet, masu jagoranci suna iya bautawa masu yawon shakatawa cikin harsuna daban daban..
An ce, yanzu yawan mutanen da suke aikin ba da hidima cikin harsunan waje yana ta karuwa, haka kuma mutane suna kara nuna sha'awa kan koyon harsunan waje. 1 2
|