Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-04-15 18:50:17    
Masu yawon shakatawa ba za su gamu da matsalar harsuna ba a Tibet

cri

Ko da yake an taba shan wahalar tashe-tashen hankula a birnin Lhasa, babban birnin jihar Tibet mai cin gashin kanta ta kasar Sin a watan Maris na wannan shekara, amma duk da haka yanzu kura ta kwanta a wannan jiha, kuma za a sake bude kofar jihar Tibet ga masu yawon shakatawa tun daga ran 1 ga watan Mayu na shekarar da muke ciki. Wadanda suke yin bulaguro a jihar Tibet ba za su gamu da matsalar harsuna ba a jihat Tibet.

Titin Barkhor da ke birnin Lhasa, hanya ce da ke kewayen gidan ibada na Jokhong, haka kuma shi ne cibiyar kasuwanci mafi wadata a wannan birni. Kullum a kan ga masu yawon shakatawa da suka zo daga ko ina a duniya, fatansu na shan bamban da juna sosai.

A cikin wani kanti da ake sayar da zane-zanen Tangkar, wato irin zane-zanen musamman na gargajiya ne na addini da aka nannade, bayan da aka yi musu ado tare da siliki masu launuka daban daban, an rataya su domin yin ibada, mai kantin ya iya yin ciniki da masu saye-saye na kasashen waje da Turanci. Mai kantin ya gaya mana cewa, shi da ma'aikatan kantinsa dukkansu sun iya tuntubar masu saye-saye da Sinanci da harshen kabilar Tibet da kuma Turanci. Sa'an nan kuma, a kantinsa akwai takardun musamman a Turance game da al'adun kabilar Tibet da ma'anar musamman ta zane-zanen Tangkar, shi ya sa ba a kasancewa da matsala ko kadan a tsakaninsu da masu saye-saye na kasashen waje a lokacin da suke yin mu'amala da juna.

1 2