Yanzu kawo wa Sanya ziyara domin kyautata lafiyar mutane ya kara jawo sha'awar mutane a kai a kai. Bisa binciken da hukumar kiyaye muhalli ta kasa da kasa ta yi wa muhimman birane 158 na kasashe 45 na duniya, Sanya ta zama ta biyu a duk duniya saboda ingancin iska mai kyau bayan birnin Havana na kasar Cuba. Watakila wannan shi ne muhimmin dalilin da ya sa Sanya ta jawo dimbin masu yawon shakatawa na gida da na waje.
Bisa kididdigar da aka yi, an ce, a shekarar bara, yawan masu yawon shakatawa da suka kawo wa Sanya ziyara daga ketare ya wuce 500,000, wato ke nan ya karu fiye da kashi 30 cikin dari bisa na shekarar 2006, ta haka saurin karuwar wannan adadi ya zama na farko a tsakanin dukkan biranen kasar Sin.
Bisa manufofin musamman da gwamnatin tsakiya ta kasar Sin ke aiwatarwa a Sanya, yanzu masu yawon shakatawa da suka fito daga kasashe da yankuna 21 na duniya suna iya ziyarar Sanya ba tare da samun iznin biza ba. Ta gidan rediyonmu wato CRI, Mr. Zhang Qi, shugaban hukumar aikin yawon shakatawa ta lardin Hainan ya gayyaci masu yawon shakatawa na duk duniya da su kawo wa Sanya ziyara domin kara fahimta kan kyan gani irin na musamman na Sanya, wanda ke kuryar kudu a kasar Sin. Ya ce, 'Masu yawon shakatawa na kasashen waje ba za su gamu da matsala ko kadan a tsibirinmu na Hainandao ba. Za su iya yin saye-saye a kantuna marasa biyan haraji, za su sauko tsibirinmu ba tare da samun biza ba kuma cikin jiragen sama da suka yi hayarsu, za su kuma yi amfani da kadarorin nishadi irin na kasar Sin da kuma kara fahimta kan al'adun kasar Sin. A madadin hukumar aikin yawon shakatawa ta Hainan, cikin sahihanci ne nake gayyatar abokanmu na duk duniya da ku kawo wa Hainan ziyara. Tsibirin Hainan, tsibiri ne na kasar Sin a yanki mai zafi, kuma aljanna ce na yin hutu a gabashin duniya.' 1 2
|