Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-04-15 18:43:17    
Sanya, wata aljanna ce ta hutawa

cri

Birnin Sanya, wani birni ne da ke kuryar kudu ta kasar Sin, haka kuma shi birni ne daya tak na yankin zafi da ake iya yin bulaguro a bakin teku. A lokacin da ake fama da dusar kankara da kuma sanyi mai tsanani a arewacin duniya, hasken rana da bakin rairayi da sararin samaniya sun jawo masu yawon shakatawa a ko ina na duniya da su kawo wa Sanya ziyara. Shi ya sa Sanya ta kan cika da dimbin mutane kamar yadda tsibiran Hawaii na kasar Amurka da tsibirin Puji na kasar Thailand suke. Yaya ra'ayoyin masu yawon shakatawa suke?

'Mun kawo nan ziyara a karo na 3. Nufinmu shi ne numfashi danyen iska da yin bulaguro. Mu kan yi yawo da safe da kuma dare.'

'Na zama a lardin Hainan har na tsawon watanni 2. Ina son wannan wuri kwarai. Yanayi ya yi kyau, kuma mutane na da kirki. Ina jin farin ciki sosai domin ganin dimbin abubuwa masu ban sha'awa.'

A Sanya, ana iya jin farin ciki a ko ina. Za ka iya sauraren kararrawa a gidan ibada na Nanshansi, wanda shi ne gidan ibada na kuryar kudu ta kasar Sin. Za ka iya sauraren labaru na gargajiya a dab da wani dutsen da aka rubuta kalmomin 'iyakar duniya' a kai. Sa'an nan kuma, za ku iya yin alkahura a cikin ruwan teku na kudancin kasar Sin da kuma saye-sayen kayayyakin fasaha na gargajiya da 'yan kabilar Li mazauna wurin suka kera. Bugu da kari kuma, in dare ya yi duhu, gidajen nishadi a bakin tekun suna cike da murna.

A cikin wadannan gidajen nishadi, a kan ga wasu mutane suna cin danyun kaguwa suna nishadi suna kuma hira da abokansu da dangoginsu cikin murna tare da iska daga teku. Sanya ta sha bamban da sauran biranen kasar Sin da ke bakin teku, in kun yada zango a Sanya sai ka ce kana kasashen waje. A gidajen nishadi, a kan iya ganin dimbin masu yawon shakatawa na kasashen waje, wadanda suka amfani da harsuna daban daban. Sabis din kuwa sun iya Rashanci da Turanci sosai.

Ivoch Chikova Nadegda, wata 'yar kasar Rasha ta lakanci kasar Sin sosai, ta taba ziyarar birane da yawa a kasar Sin. A shekarun nan 2 da suka wuce, kusan a ko wace shekara ta kawo wa Sanya ziyara. Ta ce, 'Ko a dare, mu kan ci kasuwa, mu kan je gidajen nishadi, mu kan yi yawo a bakin teku. Mu kan dawo misalin da karfe 12 da daddare, wasu kuma misalin da karfe 3 da sassafe, duk da haka, muna iya samun mota. Mun fi samun sauki a nan, in an kwatanta ta da Rasha. Muna zama a nan cikin kwanciyar hankali.'

1 2