Ban da wannan kuma, gwamnatin kasar Sin tana dora muhimmanci kan batun ba da ilmi na 'yan kananan kabilu, yayin da firaminista Wen Jiabao na kasar yake waiwaye kan ayyukan da aka yi cikin shekaru 5 da suka wuce, ya bayyana nasarar da kasar Sin ta samu daga wannan fanni. "Jimlar kudin da gwamnatin Sin ta ware cikin shekaru 5 da suka wuce domin ba da ilmi ta kai kudin Sin wato Yuan biliyan 2,430, wato ta karu da ninki 1.26 bisa ta shekaru 5 na kafin wadannan shekaru 5. An kammala shiri cikin lokaci wato an kusan tabbatar da makasudin samun ilmi tilas na makarantu masu tsarin karatu na shekaru 9 da yaki da jahilci ga samari da manya na yammacin kasar, mun samu babban ci gaba a fannin ba da ilmi bisa daidaici."
Mr. E Yitai, dan kabilar Korea, kuma mamban majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa, kuma shugaban jami'ar kabilu ta tsakiya ya nuna yabo ga wannan ra'ayin da firayim Wen Jiabao ya bayar, ya ce, "Yanzu jami'ar kabilu ta tsakiya tana daukar dalibai 'yan kabilu 56, daga cikinsu ba ma kawai da akwai dalibai masu karatun digiri na farko ba, har ma da digiri na 2 da na 3, kuma da akwai dalibai da yawa wadanda suka zo daga jihar Xinjiang da ta Tibet da sauran wurare masu nisa ko wuraren da ke bakin iyakar kasa da 'yan kananan kabilu ke zama."
Kasar Sin wata kasa ce da ke da kabilu da yawa, daga cikinsu yawan mutane 'yan kananan kabilu ya kai fiye da miliyan 100. Sabo da dalilin tarihi da halitta da kuma zaman al'umma, ba a samu daidaituwa ba wajen bunkasa tattalin arziki da zaman al'umma a shiyyoyin kananan kabilu, har ila yau ya kasance da bambanci sosai a tsakanin shiyya-shiyya, tsakanin birane da kauyuka, kuma tsakanin kabilu daban-daban. Cikin 'yan shekarun nan da suka wuce, gwamnatin Sin ta dauki manyan matakai domin kara saurin bunkasa shiyyoyin kananan kabilu da sauran wuraren kabilu da ke yammacin kasar. Alal misali za a kyautata muhimman sharudan bunkasa tattalin arziki na jihohin kabilu masu ikon tafiyar da harkokin kansu, da daidaita matsalar yaki da talauci da sauran matsalolin da suke fi addaba 'yan kananan kabilu, da yin kokarin kyautata matsayin kimiyya da fasaha da ba da ilmi ga 'yan kananan kabilu, da sa kaimi ga inganta aikin jiyya da kiwon lafiya, ta yadda za a samu babban ci gaba wajen bunkasa shiyyoyin kananan kabilu. 1 2
|