Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-04-14 18:39:14    
Mambobi 'yan kananan kabilu na majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa sun tauna miyau kan bunkasuwar yammacin kasar Sin

cri

Kwanan baya an rufe taron shekara-shekara na majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta jama'ar kasar Sin da aka yi a nan birnin Beijing, yayin da wasu mambobi 'yan kananan kabilu na majalisar suka amsa tambayoyin da wakilinmu ya yi musu, sun yi jinjina sosai ga matakan da gwamnatin Sin ta dauka cikin 'yan shekarun nan da suka wuce domin kara saurin bunkasa shiyyoyin kananan kabilu. To jama'a masu sauraro cikin shirinmu na yau, za mu kawo muku wani bayani kan abubuwan da wadannan mamboci 'yan kananan kabilu suka fada.

Yammacin kasar Sin yanki ne da 'yan kananan kabilu masu yawa ke zama, cikin 'yan shekarun nan da suka wuce, gwamnatin Sin ta dauki matakai daban-daban don sa kaimi ga bunkasa yammacin kasar. Mr. Diwana, wakili dan kabilar Tajik wanda ya zo daga jihar Xinjiang ta kabilar Uygur mai ikon tafiyar da harkokin kanta ya bayyana cewa, "Yanzu manoma da makiyaya sukan gabatar da rasidin kudin da suka kashe kan jiyya, gwamnati ce ta mayar musu da kudin da yawansa ya wuce kashi 70 cikin 100, kuma sun biya kudin asibiti kadan da kansu."

A dukkan lokutan taron shekara-shekara na majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa na jama'ar Sin, mambobin majalisar sukan gabatar da ra'ayoyi da shawarwarinsu dangane da manufofin siyasa da batutuwa masu jawo hankulan mutane, shawarwarin da suka gabatar sun sa kaimi ga bunkasa shiyyoyin kananan kabilu. Bisa matsayinsa na rayayyen Budda na wurin ibadan Lalu, ibada mafi girma da ke yankin Linzhi na jihar Tibet, Mt. luosang Danbainima, wani tsohon mamban majalisar ya ba da shawara yau da 'yan shekarun da suka wuce game da gina filin jirgin sama na Linzhi, shawarar nan ta riga ta tabbatu a shekarar da ta gabata. "An gina filin jirgin sama a yankin Linzhi, kuma an shimfida hanyar dogo da ta hada Qinghai da Tibet. Yanzu mun sami sauki wajen tafiya zuwa jihar Tibet daga birnin Beijing da lardunan Guangdong da Fujian da sauran wurare daban-daban."

1 2