Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-04-11 20:01:05    
A tashi tsaye a duk duniya don kare wutar wasannin Olimpic

cri

Wasannin Olimpic wani dakalin wasa ne ga 'yan wasan motsa jiki na duk duniya da su bayyana tunanin Olimpic na dan Adam, kuma wani dakalin wasa ne ga jama'ar kasashe da shiyyoyi daban- daban da su kara yin mu'amala da cudanya da kuma fahimtar juna, kuma wani gagarumin biki ne ga dukkan 'yan adam. Aikin mika wutar wasannin Olimpic wani muhimmin kashi ne na wasannin Olimpic. A halin yanzu wusu mutane sun dauki wannan damar mika wutar don nuna karfin tuwo da bayyana darikarsu kan siyasa, wannan ya zama cin mutunci ne ga tunanin Olimpic, kuma raini ne ga wutar wasannin Olimpic. Wadancan 'yan aware na jihar Tibet wadanda ke jawo cikas ga aikin mika wutar wasannin Olimpic, ba shakka za su gamu da tozarta daga wajen mutanen duk duniya wadanda ke hallara a karkashin tuta mai zobba guda 5 wadanda kuma ke nuna girmama wa ga tunanin Olimpic, ba shakka bakin nufinsu na neman jawo illa ga wasannin Olimpic ba zai samu nasara ba.

Matsalar Tibet hakokin gida ne na kasar Sin, kada a sa hannu a ciki daga kasashen waje. Wasannin Olimpic na Beijing wani gagarumin bikin wasannin motsa jiki ne na duk duniya, kuma ba shi da ruwa ko kadan da kowane irin batun siyasa. Domin shirya wata gasar wasannin Olimpic tare da nasara, gwamnatin Sin da jama'arta sun ci gadon manufa da tunanin wasannin Olimpic, kuma sun yi matukar kokari, wannan hakikanin abu ne a idon kowa, kuma ya samu amincewa daga ko'ina. Dukkan danyun aikin da aka yi na neman sanya matsalar Tibet cikin wasannin Olimpic, kuma a dauki wannan matsala kamar garkuwa cikin bakin nufinsu na jawo cikas ga wasannin Olimpic, tilas ne za su fusata kuma za su gamu da la'anta sosai daga wajen Sinawa da ke babban yankin kasar Sin da kasashen ketare da mutanen kasashe daban- daban na duniya wadanda ke tsayawa kan adalci.

Mun yi farin ciki da ganin cewa, a duk inda aka sa kafa wajen mika wutar wasannin Olimpic, ta samu kyakkyawar maraba daga wajen jama'ar kasashe da na shiyyoyi daban-daban. Abun da ya faranta mana rai shi ne, dimbin gaggan 'yan siyasa da na sassan wasannin motsa jiki da jama'a fararen hula na kasashe daban-daban sun fito fili sun nuna goyon bayansu ga aikin mika wutar wasannin Olimpic na Beijing. Abun da ya fi burge mu shi ne Sinawa mazauna kasashen waje sun nuna so da aminci sosai ga wasannin Olimpic na Beijing da aikin mika wutar, sun yi babban kokari domin aikin. (Umaru)


1 2