Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-04-11 20:01:05    
A tashi tsaye a duk duniya don kare wutar wasannin Olimpic

cri

Gasar wasannin Olimpic a karo na 29 tana gaba da zuwa. Daga ran 1 ga watan Afril an fara aikin mika wutar wasannin Olimpic da ke alamanta haske da hadin kai da zumunci da zaman lafiya da kuma adalci a duk duniya. Amma cikin 'yan kwanakin nan da suka wuce, watar nan ta sha gamuwa da hani da batanci da 'yan kawo baraka na jihar Tibet suka yi bisa hanyar mikawa, wannan danyen aikin da aka yi ya gamu da kiyewa daga wajen dukkan mutanen da ke kaunar wasannin Olimpic, kuma ya gamu da la'anta daga wajen dukkan mutane da ke nuna girmamawa ga wutar.

Dimbin hakikanan abubuwa na gaskiya sun bayyana cewa, mummunan tashin hankalin da aka haddasa a ran 14 ga watan Maris a birni Lhasa da hanin da aka gamuwa da shi bisa hanyar mika wutar wasannin Olimpic a kasashe da yawa, rukunin Dalai Lama shi ne ya tayar bayan kulle-kullen da ya yi cikin tsanaki, kuma ya kirkiro ta hanyar hadin gwiwa a tsakaninta da 'yan aware na cikin kasar Sin da na waje da ita. Amma wasu kafofin yada labarai masu mugun nufi na kasashen yamma sun taka dokokin sana'arsu, kuma sun ba da labari cikin gatse, sun mai da baki fari, amma wasu 'yan siyasa na kasashen yamma sun wuce gona da iri, sun yi biris da tunanin wasannin Olimpic da ka'idar babu siyasa cikin wasan motsa jiki, kuma sun fito fili sun yi sambatun banza na kaurace wa wasannin Olimpic, lalle sun riga sun yi watsi da akidar aiki da da'a sam.


1 2