Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-04-11 16:49:30    
Sarki Huizong na daular Song ta arewa ta zamanin gargajiyar kasar Sin

cri

Sarki Huizong ya kware sosai wajen zane-zane, musamman zanen furanni da tsuntsaye, kuma ya mai da hankali sosai wajen bunkasa fasahar zane-zane, har ma ya kafa kwalejin sarauta na koyon zanen hannu, wanda ya kasance irinsa na farko a tarihin duniya, tare kuma da kafa tsarin jarrabawa, don horar da kwararrun zanen hannu.

An ce, a wata rana, wani zanen da aka yi game da furen da ake kiran "china rose" ya jawo hankalin sarki Huizong, shi ya sa ya tsaya ya tambaya, "wa ya zana shi?" An ce, wani matashi sabon zuwan kwalejin shi ya zana, sai nan da nan ya ba da umurnin ba da kyautar yabo ga saurayin, kuma ya bayyana cewa, "zana china rose na da sauki, amma kuma da wuya. Sabo da a fasaloli daban daban na shekara, har ma a lokuta daban daban na rana daya, furen da kuma ganyensa su kan canza sosai, kuma wannan zanen da aka yi ya bayyana furen china rose da ke budewa a tsakar rana na yanayin bazara sosai." Wannan labari ya nuna mana yadda sarki Huizong ke mai da hankali sosai wajen duban abubuwa.

A fannin rubutun hannu ma, sarki Huizong ya kware sosai, har ma ya kirkiro wata fasahar rubutu ta kansa, wanda ake kira "Shoujinshu".

Bayan haka, a lokacin sarki Huizong, ya yi ta tattara kayayyakin tarihi da rubuce-rubuce da kuma zane-zane, kuma ya umurci ministocinsa da su tsara lattattafai da dama game da zane-zane da fasahar rubutu, wadanda suka sa kaimi sosai ga bunkasuwar zane-zane da rubuce-rubuce a kasar Sin.

A duk tsawon rayuwarsa, sarki Huizong ya nuna matukar sha'awa ga fasahar rubutu da zane-zane da tsara wakoki da kallon rawa, amma ya kawar da ido a kan harkokin mulki, har ya danka babban nauyin kulawa da harkokin kasa a hannun wasu miyagun ministoci. A shekarar 1126, mahara na waje sun zo, sun washe fadar sarki Huizong, sun kama shi da iyalansa, sun tsare shi, sun yi masa wulakanci da azaba, har ya mutu, kuma daularsa ma ta lalace.

Amma duk da kashin da ya sha a fannin siyasa, sarki Huizong ya sami nasarori sosai a wajen cigaban fasahohin zane-zane na kasar Sin. Daga wannan fanni na al'adu, ya ba da nasa taimako.(Lubabatu)


1 2